Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi garga ɗi cewa, sakamakon ya ƙin da ake ciki yanzu zai shafi duniya baki ɗaya, ba tare da la’akari da bambancin addini, ƙabila ko matsayi na tattalin arziki ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a ranar Laraba, 18 ga Maris, Araghchi ya bayyana cewa tasirin rikicin ya riga ya fara bayyana, yana mai jaddada cewa babu wanda zai tsira daga illolinsa idan ba a ɗauki matakin dakatar da ya ƙin ba.
Ya ce, “Tasirin da wannan ya ƙi zai haifar a duniya ya riga ya fara bayyana, kuma zai shafi kowa — ba tare da la’akari da arziki, addini ko ƙabila ba.”
Ministan ya yi wannan furuci ne yayin da yake kira ga jami’an ƙasashen Yamma da su ƙara ɗaukar matakan nuna adawa da ya ƙin, yana mai cewa akwai bu ƙatar ƙara yawan muryoyin da ke ƙin wannan rikici a matakin duniya.
A cikin sa ƙon nasa, Araghchi ya ha ɗa da wasi ƙar murabus da Joe Kent, Daraktan Cibiyar Ya ƙi da Ta’addanci ta ƙasa ta Amurka, ya mi ƙa.
A cikin wasi ƙar tasa, Kent ya bayyana cewa ba zai iya amincewa da ya ƙin da ake yi da Iran ba “a bisa lamirin sa,” yana mai cewa Iran ba ta kasance wata barazana ta gaggawa ga ƙasarsa ba.
Ministan harkokin wajen Iran ya kuma lura da cewa ana samun ƙarin masu magana daga cikin jami’an Turai da Amurka da ke bayyana cewa wannan ya ƙi bai dace ba, yana mai kira ga sauran ƙasashen duniya da su bi wannan hanya ta nuna adawa.
Ya ƙare da cewa, “Ya dace sauran mambobin ƙungiyar ƙasashen duniya su ɗauki irin wannan mataki domin dakatar da wannan rikici.”
