Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da ake zargi da yi wa ƙasar Isra’ila aikin le ƙen asiri, a wani lokaci da rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta.
Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Tasnim sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a wani yankin karkara da ke yammacin birnin Tehran, a lokacin rikicin kwanaki 12 da ya ɓ arke tsakanin Iran da Isra’ila a watan Yuni.
Hukumomi sun zarge shi da bai wa hukumar le ƙen asirin Isra’ila, wato Mossad, hotuna da muhimman bayanai kan wurare masu mahimmanci na tsaro.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami da farmakin sama tsakanin ɓ angarori masu gaba da juna.
Tun bayan rikicin watan Yuni, hukumomin Iran sun cafke mutane da dama bisa zargin le ƙen asiri, yayin da rahotanni ke nuni da cewa sama da mutum 10 aka kashe kan irin wannan zargi, duk da cewa ba a tabbatar da wannan adadi a hukumance ba.
A gefe guda kuma, ƙungiyoyin kare ha ƙ ƙin ɗan Adam sun da ɗe suna sukar yadda Iran ke amfani da hukuncin kisa, suna masu cewa a lokuta da dama ana amfani da shi ne wajen mur ƙushe masu adawa da gwamnati.
Bayanai daga Majalisar ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutum 1,000 aka kashe a Iran cikin shekara guda da ta gabata, lamarin da ke ƙara janyo ce-ce-ku-ce a duniya kan yadda ƙasar ke tafiyar da tsarin shari’a.
