Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Farashin ɗanyen mai ya ƙaru a ranar Alhamis, inda farashin Brent ya kai sama da dala dala 115 kan kowace ganga, wanda shi ne mafi girma cikin sama da mako guda.
Wannan hauhawar farashi na zuwa ne bayan Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya, biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan filin iskar gas na South Pars na Iran.
Rahotanni sun nuna cewa farashin Brent ya tashi da dala $6.08, wanda ya kai kashi 5.7, zuwa $113.46 a kowanne ganga da misalin ƙarfe 8:14 na safe agogon GMT, bayan da ya kai ƙololuwar $115.10 a wani lokaci na kasuwa.
Hakazalika, ɗanyen mai na Amurka (WTI) ya tashi da cent 57 zuwa $96.89 kan kowace ganga, bayan da ya taɓ a kaiwa $100.02 a farkon cinikayya.
Masana sun bayyana cewa bambancin farashin tsakanin WTI da Brent ya ƙaru matu ƙa a cikin shekaru 11, sakamakon fitar da ajiyar mai na Amurka da kuma tsadar jigilar kaya, yayin da hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin makamashi a Gabas ta Tsakiya ke ƙara dagula kasuwar mai.
Wata masaniya a kamfanin Phillip Noɓ a, Priyanka Sachdeɓ a, ta ce rikicin da ke kara tsananta a yankin, da hare-haren kai tsaye kan ababen more rayuwa na mai, na nuna yiwuwar tangarda mai tsawo a samar da mai a duniya.
A gefe guda kuma, Iran ta bayar da garga ɗin kwashe ma’aikata kafin kai hare-haren kan wasu cibiyoyin mai a ƙasashen Saudiyya, Ha ɗa ɗ ɗiyar Daular Larabawa (UAE) da ƙatar, a matsayin martani ga hare-haren da aka kai mata.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Isra’ila ce ta kai harin kan filin South Pars, yana mai cewa Amurka da ƙatar ba su da hannu a ciki, tare da garga ɗin cewa Amurka za ta mayar da martani idan Iran ta kai hari kan ƙatar.
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Amurka na duba yiwuwar tura karin sojoji zuwa yankin domin ƙarfafa ayyukan sojinta a yakin da ake yi da Iran.
