Kotu ta bada lasisin  ɗaukar bidiyon ’yan sanda a bakin aiki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Warri na Jihar Delta ta yanke hukunci mai matu ƙar muhimmanci, inda ta tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na da cikakken ’yancin Kundin Tsarin Mulki na zaukar hoto ko bidiyo na jami’an ’yan sanda yayin da suke gudanar da aikinsu a wuraren jama’a.

Al ƙali mai shari’a, Mai Shari’a H. A. Nganjiwa, ya bayyana hakan ne yayin yanke hukunci a ranar Talata a shari’ar mai lamba FHC/WR/CS/87/2025.

A cewarsa, wajibi ne jami’an ’yan sanda su ri ƙa sanya katin suna a fili tare da nuna lambobin su na aiki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikinsu.

Kotun ta kuma yi  ƙarin haske cewa bai halatta jami’an tsaro su ci zarafin jama’a ba, ko su tsoratar da su, ko su kama su, balle su kwace wayoyi ko wasu na’urori daga hannun mutanen da ke  ɗaukar hotuna ko bidiyo na yadda suke gudanar da aikinsu a fili.

Bugu da  ƙari, kotun ta umurci a biya mai shigar da  ƙara, Ma ɗwell Uwaifo, diyyar Naira miliyan biyar saboda take hakkin sa na asali, tare da  ƙarin Naira miliyan biyu domin biyan ku ɗa ɗen shari’a.

Wannan hukunci ya  ƙara jaddada cewa ’yan Nijeriya na da ’yancin sa ido kan ayyukan jami’an tsaro ba tare da fargabar cin zarafi ko ramuwar gayya ba, matakin da ake ganin zai taimaka wajen inganta gaskiya da  ɗaukar alhaki a harkar tsaro.

Yayin da yake martani bayan yanke hukuncin, Uwaifo ya bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da gaskiya da bin doka a cikin aikin ’yan sanda.

Ya ce, hukuncin zai yi tasiri sosai wajen inganta  ƙa’idojin aikin ’yan sanda, kare ’yancin jama’a, da kuma  ƙarfafa tsarin ri ƙon amana a fa ɗin aasar nan.

A cewarsa, kotun ta yi tsokaci mai zurfi kan muhimmancin ’yancin  ɗan  ƙasa da kuma yadda jami’an tsaro za su kasance masu bin doka da oda a aikinsu na yau da kullum.

By ukarofi