Yunƙurin kafa ’yan sandan jihohi ya ƙara ɗaukar hankali a Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya karɓ i ba ƙuncin kwamitin jagoranci na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da aka kafa domin tsara tsarin kafa ‘yan sanda na jihohi.

An bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar girmamawa da kwamitin ya kai masa domin neman shawarwari da gudunmawar Majalisar Dattawa kan wannan muhimmin aiki na  ƙasa.

Tun a ranar 4 ga Maris, 2026, Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olatunji Disu, ya aaddamar da kwamitin mutum takwas da aka  ɗora wa alhakin tsara yadda za a kafa ‘yan sanda na jihohi a Nijeriya.

Kwamitin,  ƙar ƙashin jagorancin shugabansa, Farfesa Olu Ogunsakin, ya yi bayani kan aikin da aka ba su, tare da neman shawarwari daga Majalisar Dattijai domin  ƙarfafa rahotonsu da inganta tsarin da za su gabatar.

A nasa jawabin, Sanata Barau ya yaba wa Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda bisa  ƙo ƙarin da yake yi na aiki tare da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wajen tabbatar da tsaron  ƙasa, a  ƙar ƙashin manufar “Sabuwar Fata”.

Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da ri ƙon amana a cikin tsarin da ake shirin kafa, tare da gargadin a samar da hanyoyin da za su hana cin zarafi da kuma wuce gona da iri.

Sanatan ya bu ƙaci kwamitin da ya mayar da hankali wajen samar da tsari mai  ƙarfi da zai tabbatar da tsaron al’umma, tare da rage fargabar da jama’a ke da ita kan batun ‘yan sanda na jihohi.

Ya tunatar da cewa a lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a da Majalisar Dattawa ta gudanar kan gyaran Kundin Tsarin Mulkin 1999, ‘yan Nijeriya sun bayyana damuwa da tsoron da suke da shi game da kafa ‘yan sanda na jihohi, don haka dole ne a samar da tsari da zai kwantar da hankalin jama’a.

 ɗaya daga cikin  ƙudurorin da ke gaban kwamitin duba Kundin Tsarin Mulki shi ne na gyara doka domin ba da damar kafa ‘yan sanda na jihohi da na al’umma, da nufin  ƙarfafa tsaron cikin gida da ha ɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Domin tabbatar da adalci da bai wa kowa damar bayar da gudunmawa, kwamitin ya gudanar da tarukan sauraron ra’ayoyin jama’a a shiyyoyi shida na  ƙasar, inda aka bai wa duk masu ruwa da tsaki damar bayyana ra’ayoyinsu kan gyaran kundin tsarin mulki.

By ukarofi