Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Nijeriya ta karɓi kashin farko na allurai 11,520 na maganin Lenacapavir, wani sabon magani mai ɗorewa da ake amfani da shi wajen rigakafin kamuwa da cutar HIV , wanda Asusun Global Fund ya bayar.
An gudanar da bikin mi ƙa maganin ne a ranar Laraba a Babban Ma’ajiyar Kayan Lafiya ta Tarayya da ke Oshodi a jihar Legas.
Lenacapaɓ ir magani ne da ake yi sau biyu kacal a shekara, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da shi a matsayin wani ƙarin zaɓ i a cikin hanyoyin rigakafin HIɓ . Ana sa ran cewa kasancewarsa mai ɗorewa zai taimaka wajen rage matsalar mantuwa da shan magunguna kullum.
Wakilin Shirin Kula da ƙanjamau, Hepatitis da Cututtukan Jima’i na ƙasa (NASCP), Mohammed Patiko, ya bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba wajen faɗaɗa hanyoyin rigakafin HIV a Nijeriya.
Ya ce Nijeriya na cikin ƙasashe tara na farko a duniya da suka fara amfani da wannan magani, yana mai ƙara da cewa ana sa ran samun jimillar allurai 52,000, inda za a kawo ƙarin kaya a watan Mayu da Oktoba.
A cewarsa, za a raba maganin kyauta ga wasu zaɓ aɓ ɓ un mutane a ƙar ƙashin wani shirin gwaji, musamman wa ɗanda ke cikin ha ɗarin kamuwa da cutar HIV , ciki har da ma’aurata masu bambancin matsayin cutar da kuma masu sana’ar karuwanci.
Ya kuma bayyana cewa za a rarraba maganin a jihohi takwas na gwaji da suka haɗa da Kwara, Gombe, Anambra, Ebonyi, Babban Birnin Tarayya (FCT), Akwa Ibom, Kuros Riba da Benuwe.
