Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Nijeriya a yankin Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, ta fitar da muhimmin gargaɗi ga al’umma kan yiwuwar ƙaruwa hare-haren ta’addanci yayin bukukuwan ƙaramar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.
Wannan gargaɗi ya biyo bayan wasu hare-haren ƙunar baƙin wake da suka faru a birnin Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno ne, inda suka shafi yankin Kasuwar Litinin, yankin Ofishin Gona (Post Office) da kuma ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya rattaba wa hannu, sojojin sun bayyana cewa bayanan sirri sun nuna yiwuwar ƙungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP za su ƙara ƙaimi a ayyukansu, musamman a ranakun 27 da 29 na watan Ramadan.
Sanarwar ta jaddada cewa irin waɗannan lokuta na ƙarshe na Ramadan kan jawo taruwar jama’a a masallatai, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren da jama’a ke taruwa, lamarin da ke sa su zama masu sauƙin fuskantar hari.
Saboda haka, rundunar ta buƙaci al’umma da su ƙara taka-tsantsan tare da kasancewa cikin shiri, musamman a wuraren da jama’a ke taruwa. Haka kuma ta roƙi jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba, ko mutum ko motsi da ke tayar da hankali, da kuma duk wani kaya da aka bari babu mai shi.
Haka zalika, masu ibada da ke halartar sallolin dare irin su Tarawihi da Tahajjud an shawarce su da su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai yayin da ake gudanar da bincike da kula da shiga da fita a wuraren ibada.
Iyaye da masu kula da yara ma an tunasar da su muhimmancin sa ido kan ’ya’yansu, musamman a lokutan dare, domin kauce wa duk wata barazana.
Bugu da ƙari, rundunar ta yi kira ga shugabannin al’umma, malamai da shugabannin ƙungiyoyin sufuri da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan batun tsaro, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
A cewar rundunar, an riga an ƙara tsaurara matakan tsaro ta hanyar yawaita sintiri, sa ido da sauran matakan kariya a faɗin yankin domin daƙile duk wata barazana.
A ƙarshe, rundunar ta tabbatar wa al’umma cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin tabbatar da zaman lafiya har zuwa ƙarshen Ramadan da kuma bukukuwan Sallah da ke tafe.
