Mahaifi ya rasa ’ya’yansa hu ɗu a fashewar boma-bomai a Maiduguri

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani mutum ya rasa ’ya’yansa maza hu ɗu a jerin fashewar bama-bamai da suka girgiza Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano.

Fashewar, wa ɗanda suka afku a  ƙofar shiga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), da yankin Monday Market da kuma yankin Post Office, sun yi sanadin mutuwar mutane kusan 27 yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wani  ɗan kasuwa, Usman Lawan ya bayyana yadda ma ƙwabcinsa, Ba Musa, wanda ke zaune a Gwange Sabon Layi, ya rasa ‘ya’yansa hu ɗu a lamarin.

Ya ce yaran sun fa ɗa cikin hatsarin ne sa’ilin da suka je sayen tabarau na bikin Sallah.

Yayin da yake magana da wakilinmu lokacin ziyarar Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ziyarci a asibitin UMTH, ya ce:

“Muna gama bu ɗa baki, ina tura kurar itace sai fashewar ta auku, na tsinci kaina kawai a asibiti. Na rasa komai nawa a wannan harin.”

“Ya saya musu sabbin kaya da takalma, sai suka zo wurinmu don sayen tabarau na bikin Sallah. Fashewar ta kashe su duka. An binne su jiya,” inji shi.

Wani mai gadi a asibitin, wanda ya samu raunuka a hannunsa da kafafunsa, ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru:

“Ina zaune a wajen asibitin sai mutane uku suka zo kan babur. Na lura da wani abu da ban amince masa ba, sai na ce su tafi. Sun dawo karo na biyu, sa’ad da na  ƙi barinsu su shiga, sai suka jefa mini wani kwanon abinci. Ya buge ni a hannu ya fa ɗi  ƙasa, yana barazanar fashewa. Na kwanta sai na ji  ƙara mai  ƙarfi. Yayin da nake  ƙo ƙarin guduwa ciki, wani kwanon ya sake fashewa ya buge ni a kafa,” inji shi.

Wata matar da ta tsira, wadda ta rasa  ɗiyarta a fashewar, ta ce: “Muna isowa asibitin sai bam  ɗin ya tashi. Na fa ɗi, ita kuma  ɗiyata ta fa ɗi matacciya. Kanta ya fashe. Suka kai ni ciki suka fa ɗa mini ta rasu. Na yi addu’a ga Allah domin Shi ne ya  ɗauki abarsa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya ’yar wata biyar.”

By ukarofi