Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙungiyar Matasan Nijeriya (NYCN), reshen ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, Kwamared Nuhu Haruna Sani, wanda aka fi sani da Alkurkawee, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Eid-el-Fitr, inda ya yi musu fatan alheri da zaman lafiya.
A cikin sa ƙonsa na Sallah, Kwamared Alkurkawee ya bayyana muhimmancin wannan lokaci na ƙaramar Sallah a matsayin dama ta ƙara dan ƙon zumunci, yafiya da kuma taimakon juna a tsakanin al’umma, musamman bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan.
Ya kuma bu ƙaci al’ummar Giwa da su ci gaba da zama cikin ha ɗin kai da juna tare da kiyaye dokoki da ƙa’idoji domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Hakazalika, shugaban na NYCN ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ƙar ƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani da ta ƙara mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa a ƙaramar Hukumar Giwa, musamman a ɓangarorin ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya jaddada cewa ƙaramar Hukumar Giwa na da matu ƙar bu ƙatar ƙarin kulawa daga gwamnati domin inganta rayuwar al’umma da kuma bun ƙasa tattalin arzikin yankin.
A ƙarshe, Kwamared Nuhu Haruna Sani Alkurkawee ya yi addu’ar Allah ya kar ɓi ibadun Musulmi, ya kawo zaman lafiya a Nijeriya, tare da bai wa shugabanni hikima da basirar tafiyar da al’amuran al’umma yadda ya kamata.
