
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shahararren jarumin finafinan Amurka, Chuck Norris, ya rasu bayan shafe shekaru 86 a duniya.
Marigayin ya shahara sosai a masana’antar finafinai saboda ƙwarewarsa a harkar faɗa da kuma rawar da ya taka a finafinai da dama na yankin Amurka.
Mutuwarsa ta girgiza masoyansa da masu kallon fim a faɗin duniya, inda mutane da dama ke bayyana alhini da jimamin rashin sa.
Za a ci lgaba da tunawa da shi saboda gudunmawar da ya bayar a harkar nishaɗi.
Iyalansa sun bayyana cewa, “Cike da jimami muke sanar da kwatsam din rasuwar masoyinmu Chuck Norris a jiya da safe. Ga duniya, shi alamar karfi ne, amma a gare mu, uba ne mai kauna.”
A makon jiya ne jarumin ya cika shekara 86, inda ya wallafa bidiyon kansa yana wasan dambe tare da cewa: “Ni ba tsufa nake yi ba, mataki nake karawa.”
Chuck Norris ya zama zakaran duniya bayan fadansu da fitaccen jarumin nan Bruce Lee a fim din “The Way of The Dragon” a shekarar 1972.
An bayyana cewa jarumin ya kwanta rashin lafiya ne a ranar Alhamis a tsibirin Kauai da ke Hawaii kana daga bisani ya rasu.
