Ƙaramar Sallah: An yi kira ga matasan Katsina da su tashi tsaye wajen neman na kansu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gidauniyar Gwagware Musa Adamu Funtua ta yi wannan kira ta hannun shugaban ta Kwamred Mannir Suleiman a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce lokaci ya wuce na yadda za ka ga matasa suna bin yan siyasa gida gida da ofis ofis suna maula wanda hakan zubar da mutuncin ne da mutuwar zuciya.

Kwamred Suleiman ya nuna takaici kan yadda matasa suka rungumi sana’ar dillanci da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa maza da mata a jihar.

“Hakan ya kawo ƙaruwar ta’addanci da ƙaurancin a manyan birane musamman a cikin garin Katsina wannan abin takaici,”Inji Suleiman.

Mannir ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da ya ɗaukaka darajar cibiyar koyar da sana’o’i na garin Katsina da gina wasu cibiyoyi a wasu ƙananan hukumomi da ke jihar.

A cewar sa ya zama wajibi matasa su yi amfani da wannan cibiyoyi wajan faɗaɗa koyon sana’ar da suka fara a baya wanda shine mafita a gare su.

Ya ce abinda ya sani shine gwamnatin Dikko Raɗɗa ya ɓullo da shirin tallafawa waɗanda suka kammala samun horo da Kayan aiki da tallalafin jari da zai taimakawa matasa wajan buɗe wararen sana’a.

Shugaban gidauniyar ya gargaɗi matasan Arewa masu tururuwa zuwa kudancin ƙasan da su sake tunani ganin yadda matasan ke rasa rayukansu sakamakon rikice rikicen ƙabilanci.

“Ku tsaya a jihohin ku ku rungumi sanar Noma da kasuwanci domin gina kanku don ku tsira da mutuncin ku,maimakon ku tsallake zuwa kudancin ƙasar inda nan rayuwa ba tabbas”inji Kwamred Suleiman.

Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da Kwamishina Musa Adamu Funtua da manyan yan siyasa da yan kasuwa da suka taimakawa mabuƙata a cikin azumin watan Ramadan.

By ukarofi