Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Yayin da mafi yawan Musulmai a Jihar Kano suka gudanar da Sallar Eid al-Fitr a ranar Juma’a, mabiyan ɗarikar Qadiriyya sun gudanar da tasu sallar a yau Asabar a unguwar Makwarari da ke cikin birnin Kano.
Sheikh Khalifa Sheikh Sammani Yusuf Makwarari ne ya jagoranci sallar, inda ya bayyana cewa ɗarikar tasu ba ta bi umarnin Sarkin Musulmi na Sokoto ba, wanda ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar Sallar Idi.
Sarkin Musulmi na Sokoto, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar ƙoli ta harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), it ce hukuma da ake amince wajen tantance farawa da kuma ƙarshen watan Ramadan ta hanyar sahihan rahotannin ganin wata a faɗin ƙasar.
Sanarwarsa galibi ana bi a duk faɗin ƙasa domin tabbatar da haɗin kai tsakanin Musulmai.
To sai dai kuma ana samun saɓani kan ganin watan a wajen wasu ɓangarorin musulmi ko wasu rahotannin da suke fitowa daga ƙasashen maƙwabta na iya haifar da bambancin gudanar da ibadar ta Idi a tsakanin wasu malamai da al’ummomi a Arewacin Nijeriya.
