Mutuwar Mr. Moses Adokwe: Garma ta karye da sauran aiki, cewar Rev. Akwande

Spread the love

Daga JOHN DOGO WADA, a Keffi

Shugaban ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Najeriya reshen Lafia da kewaye (Institute of Chartered Accountants of Nigeria, Lafia and District Society – ICAN), Rev. Steven Thomas Akwande, ya bayyana alhininsa a madadin dukkan mambobin ƙungiyar bisa rasuwar ɗaya daga cikin su, marigayi Mista Moses Danladi Adokwe, wanda ya ce rasuwarsa ta girgiza ƙungiyar matuƙa.

Rev. Akwande ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa da aka rabawa manema labarai, ciki har da wakilinmu a Keffi, hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.

Ya ƙara da cewa rasuwar marigayin ta zo ne a daidai lokacin da yake gab da zama sabon shugaban ƙungiyar karo na 8 a watan Nuwamba na shekarar 2026. Ya bayyana cewa marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban a ƙungiyar, ciki har da sakataren kuɗi, ma’aji, babban sakatare, sannan a halin yanzu mataimakin shugaban ƙungiyar na reshen Lafia da kewaye.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Allah ya karɓi rayuwarsa daga gare mu, kuma tabbas mun yi babban rashi, domin samun ƙwararren akanta irin sa ba ƙaramin aiki ba ne.

“Duk da haka, a matsayinmu na masu tawakkali ga Allah, mun yarda cewa Ubangiji da ya halicce shi ne ya san dalilin ɗaukar rayuwarsa.”

Ya ci gaba da cewa, a madadin dukkan mambobin ƙungiyar ƙwararrun akantoci (ICAN), musamman shugaban ƙasa, Mallam Haruna Nma Yahaya, mni, Ph.D., FCA, da kuma shugaban reshen Nasarawa karo na 7, Rev. Steven Thomas Akwande, tare da sauran shugabanni da mambobi baki ɗaya, suna miƙa sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokansa, shugabanni, da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), inda suka roƙi Allah ua jiƙansa, ya gafarta masa, kuma ya sa Aljanna ce makomarsa.

By ukarofi