Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyar ADC ta jefa tambaya kan yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka ce an samu bayan cire tallafin man fetur, tana mai cewa farashin mai ya ƙaru da kusan kashi 500 cikin 100 tun bayan rantsar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023.
Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani ga sukar da jam’iyyar APC ta yi wa ADC.
A martaninta, APC ta zargi jam’iyyar adawa da yaɗa bayanan ƙage kan danganta ƙaruwar talauci zuwa kashi 63 cikin 100 ga gwamnatin Tinubu.
Wani bincike da aka gabatar a wani taron masu ruwa da tsaki da cibiyar Agora Policy ta shirya a Abuja ya nuna cewa adadin ‘yan Nijeriya da ke fama da talauci ya tashi daga kusan kashi 49.8 zuwa kimanin kashi 63 bayan cire tallafin mai, kafin ya ɗan sauka kaɗan sakamakon wasu shirye-shiryen tallafin jinƙai da gwamnati ta ƙaddamar.
Abdullahi ya ce, jam’iyyarsa ba ta ƙirƙiri alƙaluman ba, illa kawai ta fito da bayanan da suke a fili kan halin tattalin arzikin ƙasar. Ya ƙara da cewa rahotanni masu zaman kansu sun nuna cewa miliyoyin ‘yan Nijeriya sun faɗa cikin talauci tun bayan fara aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki.
A cewarsa, bincike ya nuna cewa kashi 93 cikin 100 na ’yan Nijeriya na ganin ƙasar na tafiya a akasin hanya, yayin da kashi 88 suka bayyana tattalin arzikin ƙasa a matsayin mara kyau. Haka kuma, kashi 74 sun ce rayuwarsu ta yau da kullum ta taɓarɓare sosai.
Abdullahi ya jaddada cewa waɗannan ba kalaman ’yan adawa ba ne, illa ra’ayoyin jama’ar ƙasa baki ɗaya, ciki har da mambobin APC. Ya kuma yi watsi da iƙirarin gwamnati cewa wahalar da ake ciki ta wucin gadi ce, yana mai cewa alƙaluma sun nuna akasin haka.
Ya ce, bincike ya nuna cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun shafe shekarar da ta gabata suna fama da rashin abubuwan more rayuwa. Kashi 82 sun ce sun sha fama da rashin isasshen abinci, haka nan adadi iri ɗaya sun ce sun rasa damar kula da lafiya. Kashi 79 sun ce sun yi fama da rashin man girki, yayin da kashi 74 suka ce sun rasa ruwan sha mai tsafta. Haka kuma, kashi 95 sun ce sun taɓa zama ba tare da kuɗin shiga ba a wani lokaci a cikin shekarar.
Dangane da farashin mai, Abdullahi ya ce tun bayan hawar Tinubu mulki a watan Mayun 2023, farashin litar fetur ya tashi daga kimanin naira 255 zuwa kusan naira 1,500 a sassa da dama na ƙasar. Ya ce ƙarin farashin ya haddasa tashin kuɗin sufuri da na abinci, wanda ya ƙara jefa talakawa cikin mawuyacin hali.
Ya kuma tambayi yadda ake amfani da kimanin naira tiriliyan 6.4 da aka ce an tanada daga cire tallafin mai. A cewarsa, jama’a na son sanin inda kuɗin ke tafiya idan har ana cewa ana karkatar da su zuwa muhimman sassa na ci gaban ƙasa.
Abdullahi ya yi tambaya mai muhimmanci: idan ana amfani da kuɗaɗen don inganta rayuwar jama’a, me ya sa ‘yan kwangila na cikin gida ba sa samun biya, kuma me ya sa jami’o’i har yanzu ba su da kayan aiki na zamani?
