Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen 2027 da su ajiye muƙamansu kafin ko a ranar 31 ga Maris.
Umarnin ya dogara ne da tanadin Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, tare da jadawalin da INEC ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu wadda Babban Sakatare na GSO, Ibrahim Kana, ya fitar an bayyana cewa umarnin ya shafi dukkan nau’ikan masu riƙe da muƙaman siyasa na shugaban ƙasa da ke son tsayawa takara ko neman tikitin jam’iyya.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da: Ministoci da Ministocin Jihohi, Masu ba shugaban ƙasa shawara (Special Adɓisers); Manyan mataimaka na musamman (Senior Special Assistants); Mataimaka na musamman (Special Assistants) da Mataimaka na kai tsaye (Personal Assistants)
Sauran sun haɗa da: Daraktoci Janar (Directors-General); Shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati.
An buƙaci dukkan waɗanda abin ya shafa da su miƙa takardun murabus dinsu ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya kafin wa’adin 31 ga Maris.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan mataki yana da muhimmanci domin tabbatar da bin dokokin zaɓe, ƙara gaskiya a harkokin siyasa, da kuma samar da daidaito ga duk masu neman takara gabanin zaɓen 2027.
Haka kuma, ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su bi wannan umarni ba tare da saba wa shi ba, yana mai tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa dimokuraɗiyya da gudanar da sahihin zaɓe a Nijeriya.
