Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Jam’iyyar APC a jihar Kano ta musanta zargin da ake yi mata cewa tana da hannu a harin da aka kai wa mambobin NNPP a mazabar Ruwan Bago da ke ƙaramar hukumar Rogo.
Hakan ya biyo bayan zargin da NNPP ta yi cewa wasu ’yan daba da ake zargin suna goyon bayan APC ne suka kai wa mambobinta hari yayin wani taron siyasa da aka gudanar a yankin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, reshen APC na jihar Kano ya bayyana zargin a matsayin marar tushe, yana mai cewa NNPP na ƙoƙarin jefa APC cikin abin da jam’iyyar ta kira rikicin cikin gida na NNPP.
Sanarwar, wadda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ya sanya wa hannu, ta ce APC jam’iyya ce mai bin doka da oda wadda ta himmatu wajen gudanar da siyasa cikin lumana, kuma ba ta taɓa amincewa da tashin hankali kan mambobin kowace jam’iyyar siyasa ba.
Jam’iyyar ta kuma ce abin mamaki ne yadda NNPP ta zargi APC maimakon ta mayar da hankali wajen magance rikice-rikicen cikin gida da ake zargin suna tasowa sakamakon sauya sheka da sabbin tsare-tsaren siyasa a cikin jam’iyyar.
Duk da musanta zargin, APC ta bayyana cewa tana goyon bayan kiran da ake yi na gudanar da cikakken bincike ba tare da son zuciya ba kan abin da ya faru daga hukumomin tsaro.
Jam’iyyar ta bukaci hukumomi su tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ta siyasa ba.
Haka kuma APC ta roƙi ’yan siyasa a jihar su yi taka-tsantsan wajen furta kalamai domin kauce wa tayar da rikici tsakanin magoya baya.
