Rundunar ‘yan sanda ta yi ƙarin haske game da rarraba sassa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Sufeto Janar na rundunar, Olatunji Disu ya umarci a rarraba dukkan sassan jami’anta da ke manyan ofisoshinta na jihohi.

A wata sanarwa da ta aike wa ‘yan jarida ta hannun Kakakinta Anthony Placid, rundunar ‘yan sandan ta bayyana rahotannin a matsayin “rashin fahimtar haƙiƙanin abin da umarnin sufeton ya ƙunsa”.

A cewarta, wasu gidajen jarida sun yi ikirarin cewa sufeton ya umarci a gaggauta rarraba sassa jami’ai na musamman, wanda hakan ba shine abin da ake nufi ba.

Ta bayyana cewa, Sufeto Janar Disu ya kula da yadda al’umma ke nuna damuwa akan ayyukan jami’an sassa wanda ke zama takura a gare su kamar yadda ya yi la’akari da ƙoƙarinsu wajen yaƙar aikata manyan laifuka.

Akan haka ne ya umarci da a rarrage jami’an sassa da na matakin jihohi zuwa biyar-biyar, sai kuma na yanki da ofishi zuwa uku-uku.

A cewar rundunar, aiwatar da matakin zai yiwu ne ta hanyar haɗewa da rarraba sassa ta yadda za su dace da tsarin da al’umma ba za su riƙa kokawa akan ayyukansu ba.

Kazalika, rundunar ta ce sauyin bai shafi jami’an da jihohi suka samar ba kamar su LSRRS a Legas, SRS a Oyo da DOO-AKPOR a Bayelsa da makamansu.

By Babaji