
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ɗan wasan ƙungiyar Manchester City, Rodri ya ƙarfafa raɗe-raɗin cewa akwai yiwuwar ya koma Real Madrid ta ƙasar Sifaniya, yana mai cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen amsa tayin gwarzuwar ƙungiyar.
Rodri, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2024, ya bayyana haka ne yayin wata hira da Onda Cero, inda ya yi bayanin makomar gobensa a harkar ƙwallon ƙafa duba da yadda wa’adin kwantaraginsa a filin Etihad ke gab da ƙarewa.
Ya bayyana cewa, duk da ya shafe tsawon shekaru huɗu a baya yana taka wa Atletico Madrid tamola, hakan ba dalili ba na cewa ba zai koma Madrid ba a matsayinta na gwarzuwa a Turai.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Manchester City ke shirin tattaunawa da ɗan wasan akan batun sabunta kwantaragin nasa a ƙungiyar yayin da kakarsa ta ƙarshe ke gabatowa.
Saidai ɗan wasan ya nuna sha’awarsa ta sauya sheƙa zuwa Santiago Bernabéu da kuma burinsa na koma wa ƙasarsa, wanda ya sanya Real Madrid cikin shirin ko ta-kwana.
A cewar rahotanni daga The Athletic da kafafen labarai da dama na Sifaniya, Los Blancos ta bayyana ɗan shekara 27 ɗin a matsayin wanda take nema a sahun farko na ‘yan wasan tsakiya cikin waɗanda za su maye gurbin da wasu taurarinta suka bari tun a kakar da ta gabata.
