
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata haɗakar tawaga ta masu ruwa da tsaki ta yi alla-wadai da abin da ta kira da faɗaɗa salon zargin kame da tozarta ‘yan jaridar a jihar Neja, tana mai kira ga Gwamna Umaru Mohammed Bago da ya girmama hukuncin ‘yancin doka da kiyaye ƙa’idodin dimukraɗiyya.
A wata takarda da Mataimakin jagoranta na ƙasa kuma Kodinetan North Movement na Arewa maso Yamma, Sani Ahmed Zangina ya fita a ranar Laraba, ƙungiyar ta koka da rahotannin gidajen jarida akan yadda ake tauye ‘yancin masu aiki a fannin a ƙarƙashin gwamnatin jihar ta yanzu.
Acikin takardar, an zargi gwamnatin Neja ta take ‘yancin bayyana ra’ayi da ‘yancin aikin jarida, tana mai gargaɗin faruwar ire-iren haka ka iya zama barazana ga tsarin mulkin dimukraɗiyya matuƙar ba a yi nazari a kai ba.
Akan haka ne ƙungiyar ta yi kira ga Gwamna Bago da yakiyaye hukunce-hukuncen doka duab da cewa kowane ɗan Nijeriya yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa da kuma ‘yaɗa labarai.
Ta bayyana cewa, dimukraɗiyya na bunƙasa ne a inda ake martaba mabanbanta ra’ayoyi da bai wa al’umma suka yayin da suka ga gazawar gwamnati.
Haka kuma, ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa wajen tabbatar da martabobin dimukraɗiyya ciki har da jure wa sukar ‘yan adawa da damawa da ɓangarorin daban-daban.
