Daga UMAR GARBA a Katsina
Wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Jibrin Tanimu, ya rubuta wa gwamnan Katsina ta hanyar lauyoyinsa wani ƙorafi a kan yadda jami’an Hizba ta jihar Katsina suka shiga gidansa a ranar 10 ga watan Maris da misalin ƙarfe 1:20 na dare, suka ɓalle ƙofofin gidansa, suka tayar wa da iyalansa hankali. Sannan cikin daren suka tafi da shi bisa zargin wani ƙorafi a kan maganar yarjejeniyar kasuwanci da aka kawo musu.
A takardar da lauyan ɗan kasuwan ya rubuta wa gwamnan Katsina, ya yi ƙorafin cewa jami’an Hizba sun saɓa wa duk wata doka ta ƙasa da ta bincike da kuma ta tuhuma, da dokokin da suka kafa ta, na shiga gidan wannan ɗan kasuwa da tsakar dare.
A takardar ƙorafin sun ce ‘yan Hizban sun je gidansa su 25, kuma bayan sun ɗauko shi, sai da suka yi ta yawo da shi cikin Katsina kafin suka kai shi ofishinsu.
Lauyan ya ƙara da cewa ya je har ofishin Hizba ya faɗa musu cewa koken da aka kawo musu game da ɗan kasuwar yana gaban kotu, kuma an saka ranar 25 domin cigaba da shari’ar, don haka su sake shi.
Lauyan ya ƙara da cewa har ma kotun da ke sauraren shari’ar, Upper Shari’a Court 11, ta aika wa Kwamandan Hizba ta jiha wasiƙar cewa wannan shari’a tana a gabanta, don haka a saki Jibrin Tanimu da suka kama. Amma maimakon su sake shi, sai suka sanya shi a mota suka kai shi Jihar Kano inda suka ce daga can aka aiko musu da ƙorafin, wanda a can Kano ne aka sake shi.
Majiyar Manhaja ta Jaridar Katsina Times ta tuntuɓi hukumar Hizba game da lamarin, wani wakilin hukumar Alhaji Muhammadu Maslaha,
ya tabbatar da zuwa gidan Alhaji Jibrin da dare. A cewar shi umurni ne suka samu daga wata kotu domin a tisa ƙeyar ɗan kasuwar zuwa Kano.
Ya ce sun neme shi ba su same shi ba, shi ya sa suka je gidansa da dare.
Ya ce, “Da farko da muka buga masa ƙofa muka ce jami’anmu ne, sai ya fara ihu ɓarayi.”
“Da muka shiga gidan, iyakar mu farfajiyar gidansa, babu wanda ya shiga cikin falonsa balle ɗakunan gidansa.
Alhaji Muhammadu ya ce, “Lamarin bincike ne na zargin karɓar kuɗin wasu da niyyar za a samar musu aiki, aka kuma ba su takardar bogi ta aiki. Mutanen suka nemi a maido musu da kuɗin su. Mutanen suka shigar da ƙara a Kano, daga can Kano aka nemi a kawo shi. Da yake lamarin ya shafi wani daga cikin ‘yan Hizba namu, shi ya sa muka je muka ɗauko shi muka kai shi Kano kamar yadda aka umurce mu.” In ji shi.
Sai dai Alhaji
Jibrin ya musanta zarge-zargen Hizba a kansa. Ya faɗa wa majiyarmu cewa matsalarsa ta yarjejeniyar kasuwanci ce da wasu mutane kuma bai saɓa ba.
“Amma a lokaci guda masu kuɗin suka nuna son kuɗinsu, kama-kama maganar har ta je kotu, kuma ana kotu,” in ji shi.
