Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mazauna ƙauyen Bargaja da ke ƙaramar Hukumar Isa a jihar Sakkwato sun bayyana tsananin damuwa da fargaba sakamakon ƙaruwar hare-haren da ake dangantawa da fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, inda suka ce sun gaji da irin halin da suke ciki na rashin tsaro da tashin hankali.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadin da ta gabata, wasu gungun maharan sun kai hari ƙauyen, inda suka tilasta wa mazauna tserewa daga gidajensu bayan sun ba su wa’adin barin yankin ko kuma su fuskanci mutuwa.
Wannan lamari ya ƙara nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara muni a yankunan Sakkwato, Zamfara da sauran jihohin makwabta.
Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mata da yara ke ta faman lodin kayansu cikin mota domin tserewa, cikin wani yanayi mai cike da firgici da tashin hankali. A cikin bidiyon, an ji wani namiji yana kuka cikin harshen Hausa, yana cewa sun gaji da hare-hare da kashe-kashe, kuma ba su da wani zaɓi illa barin garin domin tsira da rayukansu.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, abin da ya jefa jama’a cikin firgici, inda da dama suka tsere zuwa birnin Sakkwato da wasu ƙauyuka makwabta domin neman mafaka.
ƙauyen Bargaja, wanda a da ya yi suna wajen noma dankalin turawa, waken soya da kiwon dabbobi, ya koma tamkar inuwa ne kawai sakamakon yawan hare-haren da ake kai masa a ’yan shekarun nan.
Wani masani kan harkokin tsaro, Bashiru Altine Giyawa, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa ƙauyen na daga cikin wuraren da suka daɗe suna ƙoƙarin tsayayya da ’yan bindiga. Ya ce jami’an sa-kai sun fafata da maharan a wani mummunan artabu, amma abin takaici, mutum biyu daga cikinsu sun rasa rayukansu. An bayyana sunayensu da Umaru Biri da Garba Mumminu.
Duk da wannan hali, kwamandan rundunar soji ta 8 Diɓision ya ce sojoji sun shawo kan wasu mazauna da kada su bar yankin, tare da ba su tabbacin cewa za a ƙara tsaurara matakan tsaro. Sai dai da dama daga cikin al’ummar yankin ba su gamsu da wannan tabbaci ba, ganin yadda hare-hare, garkuwa da mutane da satar dabbobi suka zama ruwan dare.
Manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu, yayin da mata da yara ke fama da wahalhalun gudun hijira da ƙarancin ababen more rayuwa. Haka kuma, ƙauyuka makwabta kamar Tidibale da Katanga sun fuskanci irin waɗannan hare-hare, abin da ke ƙara haifar da tsoro a yankin.
Shugabannin al’umma sun yi gargaɗin cewa lamarin na iya rikiɗewa zuwa babbar matsalar jin kai idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, domin yana da illa mai tsanani ga tattalin arziki da zamantakewar jama’a.
Duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke yi na tunkarar maharan, ƙarfin su da sauƙin motsinsu na ci gaba da zama babban ƙalubale, yayin da al’ummar yankin ke ci gaba da fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa.
