Kwamishinan ’yan sandan Legas ya gargaɗi rundunar haɗin gwiwa kan take haƙƙi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Legas, Olohundare Moshood Jimoh, ya yi kakkausar gargaɗi ga jami’an rundunar musamman da ke kula da muhalli da laifuffuka na musamman, wato State Taskforce on Enɓironmental and Special Offences, biyo bayan koke-koken jama’a kan zargin take haƙƙin ɗan Adam da ake dangantawa da ayyukansu na tabbatar da doka.

Wannan gargaɗi ya biyo bayan wata muhawara da ta karaɗe kafafen sada zumunta, bayan yaɗuwar wani rahoto da ya shafi wani direba mai suna Lateef Adeyemo, wanda aka kama bisa zargin tuƙin mota a saɓanin hanya. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke zargin rundunar da wuce gona da iri wajen aiwatar da aikinsu.

Yayin da yake jawabi bayan wani taron horaswa da aka shirya wa jami’an rundunar a hedikwatar ’yan sanda da ke Ikeja, kwamishinan ya bayyana cewa an tunatar da jami’an muhimmancin gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa tare da mutunta haƙƙin ’yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, wannan horaswa na cikin ƙoƙarin ƙarfafa ladabi da tabbatar da cewa duk wani aiki na aiwatar da doka yana tafiya daidai da tanade-tanaden shari’a tare da kare mutuncin bil’adama.

Kwamishinan ya bayyana cewa binciken bidiyon da aka samu dangane da lamarin bai nuna wata shaida ta cin zarafi ko wulaƙanci ga wanda aka kama ba, yana mai cewa an bi hanyoyin da suka dace wajen kama shi.

Sai dai ya jaddada cewa duk wani jami’i da aka tabbatar ya aikata laifi ko wuce gona da iri zai fuskanci hukunci mai tsanani, har da yiwuwar rusa rundunar baki ɗaya. Ya nanata cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma ba za a lamunci duk wani nau’in cin zarafi ba.

Game da batun direban, kwamishinan ya ce an gurfanar da shi a gaban kotun tafi-da-gidanka jim kaɗan bayan kama shi, inda aka ba shi beli, amma daga bisani aka tsare shi bayan ya kasa cika sharuɗɗan belin.

Ya kuma bayyana cewa dukkan matakan da aka ɗauka sun yi daidai da dokokin Jihar Legas da ke kula da laifuffukan muhalli da zirga-zirga, tare da ƙaryata zargin cewa an kama shi ba bisa ƙa’ida ba.

By ukarofi