Sojoji kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen ta’addanci ba – Buratai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Babban Hafsan Sojin ƙasa na Nijeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa ba za a iya kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan ba ta hanyar dogaro da sojoji kaɗai, yana mai gargaɗin cewa irin wannan hanya na iya raunana zaman lafiya na dogon lokaci.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talbijin na Channels, inda ya jaddada cewa dukkan ɓangarorin gwamnati da al’umma na da rawar da za su taka wajen magance matsalar tsaro.

Ya ce, yawan jingina komai ga sojoji kuskure ne, domin a cewarsa, ba aikin sojoji ba ne su bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci ko kuma su ɗauki dukkan matakan da suka shafi siyasa da tsare-tsare.

A cewarsa, akwai hukumomi na musamman da ke da alhakin bincike da daukar mataki kan irin waɗannan batutuwa, kuma abin da ya kamata shi ne a bi diddigin su tare da ɗaukar matakan doka.

Tsohon hafsan ya ƙara da cewa, rawar da sojoji ke takawa tana iyakance ne da abin da kundin tsarin mulki ya tanada, yayin da manyan shawarwari kamar yadda za a kula da ’yan tawayen da suka tuba ke hannun gwamnati.

Ya bayyana matsalar ta’addanci a Nijeriya a matsayin mai sarƙaƙiya kuma mai tushe mai zurfi a cikin al’umma, yana mai cewa ba za a iya magance ta cikin gaggawa ko kuma da ƙarfin bindiga kaɗai ba.

A cewarsa, matsalar ta shafi aƙida da tunanin wasu mutane, wanda ke buƙatar haɗin kai da dabaru daban-daban domin shawo kanta.

Buratai ya yi nuni da cewa, a lokuta da dama ana ɗora wa sojoji nauyin da ya wuce ƙarfin aikinsu, inda ake tsammanin za su share dukkan ’yan ta’adda cikin ɗan lokaci, alhali kuwa matsalar tana buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, hukumomi da kuma al’umma baki ɗaya.

A wani ɓangare kuma, an tuna cewa a watan Maris na shekarar 2024, gwamnatin tarayya ta bayyana gano wasu mutane da kamfanoni da ake zargi da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci, ciki har da wasu masu sana’ar canjin kuɗi. Duk da haka, har yanzu ba a samu cikakken bayani kan matakan shari’a da aka ɗauka a kansu ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

Masana na ganin cewa kalaman Buratai sun sake jawo hankali kan buƙatar ɗaukar matakai masu faɗi da suka haɗa da tattalin arziki, ilimi, da kuma wayar da kan al’umma domin magance matsalar tsaro mai ɗorewa a Nijeriya.

By ukarofi