
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja domin tattaunawa akan muhimman batutuwan ƙasa da ƙasa.
Ziyarar na zuwa ne bayan ganawarsu ta baya a birnin N’Djamena a lokacin rantsar da shugaban Chadi, wanda Tinubu ya halarta a ranar 23 ga Mayu, 2024.
Masana harkokin difulomasiyya na ganin cewa wannan ganawa za ta ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Nigeria da Chad, musamman a fannonin tsaro, yaƙi da ta’addanci, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel.
Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna akan yadda za a inganta haɗin-gwiwar soji da musayar bayanan sirri domin daƙile barazanar ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar sassan ƙasashensu.



