Gwamna Raɗɗa ya taya FRCN murnar cika shekaru 75 da kafuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya gidan rediyon Nijeriya murnar cika shekaru 75 da kafuwa.

Gwamnan ya yaba wa shugabanni da ma’aikatan kafar yaɗa labaran bisa shekaru 75 na sadaukar da kai wajen yi wa ƙasa hidima.

“Gidan Rediyon tarayya (FRCN) ta kasance ginshiƙi wajen yaɗa bayanai da kuma ci gaban ƙasa tsawon shekaru 75. Kun ilmantar da miliyoyin jama’a, kun sanar da miliyoyi, kuma kun nishaɗantar da miliyoyi,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da rediyo ke takawa wajen isa ga ‘yan Najeriya a faɗin ƙasa, inda ya ce FRCN ta ci gaba da kasancewa muryar amana da kuma tushen sahihan labarai da nishaɗi ga al’umma tsawon lokaci.

“Rediyo na ɗaya daga cikin hanyoyin sadarwa mafi ƙarfi a Najeriya. FRCN ta kiyaye martabar wannan fanni. Kun nuna ƙwarewa da riƙon amana a aikinku,” in ji gwamnan.

Gwamna Raɗɗa ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga kafar yaɗa labaran da ta ci gaba da wannan muhimmiyar hidima, tare da dacewa da sauye-sauyen zamani ba tare da kaucewa babban burinta na yi wa jama’a hidima ba.

A madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, gwamnan ya yi wa FRCN fatan alheri da nasara a ayyukanta na gaba, tare da addu’ar samun ƙarin shekaru na hidima mai tasiri ga ƙasa.

By ukarofi