
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta ADC a Nijeriya ta buƙaci a cire Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Joash Amupitan daga muƙamin.
ADC ta ce hukumar ta koma kamar ‘yan amshin shatar jam’iyya mai mulki, wato APC don haka ba za ta iya amincewa da hukuncin hukumar ba a zaɓen 2027.
Da fari, INEC ta cire sunan Sanata David Mark da Abdulra’uf Aregbesola a matsayin shugaba da babban sakataren jam’iyyar daga shafinta na yanar gizo.
A sanarwar da ta fitar ranar Laraba, INEC ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya ta Abuja game da rikicin da ake yi tsakanin tsagin su David Mark da kuma na su Nafi’u Gombe akan shugabancin hukumar.
A wani taron manema labarai ƙarkashin jagorancin Sanata David Mark, jagororin ADC sun ce hankalin jam’iyyar bai kwanta ba da shugabancin INEC bisa take-taken akan al’amuransu.
Don haka ne jam’iyyar ta buƙaci a tsige Farfesa Amupitan a matsayin shugaban hukumar ba tare da ɓata lokaci ba tare da sauran kwamishinonin zaɓe na ƙasa.
A cewar ADC, hukumar ba za ta iya gudanar da sahihin zaɓe ba matuƙar ba a sauya tawagar jagorancin al’amuranta ba.
Kazalika, jama’iyyar ta yi watsi da matakin da INEC ta ɗauka inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da harokokinta kamar yadda ta saba a baya cikin tsari da kiyaye doka da oda.
