Kotu ta yi watsi da ƙarar Sowore akan DSS da wasu bisa wallafar Tinubu ta Facebook

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya ya yi watsi da ƙarar kare haƙƙin ɗan-adam da Omoyele Sowere ya shigar akan Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, darakta janar ɗinta da kuma dandalin Meta da aka fi sani da Facebook.

Da yake gabatar da hukunci, Alƙali Umar ya ce babu ɗaya daga cikin buƙatu uku da Sowore ya gabatar da suka cancanci a biya don haka ya yi watsi da ita a sakamakon rashin nagarta.

Sowore ya yi ikirarin cewa dandalin Facebook ya yi aiki da umarnin DSS wajen sauke rubutun da ya yi akan Tinubu a ranar 25 ga watan Agustan 2025, inda ya kira shi da “ɓarawo”, lamarin da ya sa kuma aka rufe shafinsa (Sowore).

A cewarsa, goge rubutun da rufe masa shafi da kamfanin Meta ya yi ya ci karo da ‘yancinsa na sauraron bayani, bayyana ra’ayi da makamansu.

Mai Shari’ar ya ce, ikirarin Sowore bai da alaƙa da tauye masa ‘yancin sauraren bayaninsa bisa adalci a ƙarƙashin hanyoyin aiwatar da dokokin ‘yancin ɗan-adam.

Ya bayyana cewa, ƙorafin da DSS da darakta janar ɗin nata suka yi wa Meta dangane da wallafar Sowore ya saɓa wa dokokin Nijeriya kuma hakan ba tauye masa ‘yanci ba ne.

By Babaji