Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ficewar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, daga muƙaminsa na Shugaban Kwamitin Amintattu na Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya da ficewarsa da jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya da jihar ta Kano da kuma shigarsa jam’iyyar ADC ta adawa sun haifar da sabon yanayi na ruɗani a farfajiyar siyasa Kano da ma Arewa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gawuna ya ajiye muƙaminsa ne a ranar 27 ga Maris, 2026, bisa umarnin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya buƙaci duk masu riƙe da muaaman siyasa su sauka, domin shirin zaɓen shekarar 2027, kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Sai dai duk da cewa, matakin na iya zama kamar na bin doka ne kawai, majiyoyi daga cikin jam’iyya sun nuna cewa, akwai wani babban sauyi na siyasa da ke shirin faruwa a Kano, wanda zai iya sauya tsarin ƙarfin iko a jihar mai cike da tasirin siyasa a Nijeriya.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Gawuna ya gode wa Shugaban ƙasa Tinubu bisa damar da aka ba shi, yana mai cewa, ya yi aiki ne cikin mutunci da kishin ƙasa. Haka kuma ya bayyana cewa, ya miƙa makomar siyasarsa “a hannun Allah” tare da tabbatar da cewa, zai sauka cikin lumana.
Sai dai majiyoyi da dama sun nuna cewa, wannan mataki ba ƙaramin shiri ba ne, dom in jim kaɗan bayan saukar tasa sai ya fice daga APC, sannan ya kai ziyara ga jagoran siyasar adawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shine jagoran tafiyar Kwankwasiyya, sannan a washegari yanki katin shaidar ADC, wanda hakan ke alamta cewa, zai nemi takarar gwamna ne a jam’iyyar.
Wannan sauya sheƙa ya janyo farin ciki a ɓangaren magoya bayan Kwankwaso, yayin da ya haifar da damuwa a cikin APC. Ana ganin wannan mataki na daga cikin dabarun tunkarar zaɓen gwamnan Kano na 2027, inda Gawuna zai iya zama babban abokin hamayya ga gwamna mai ci a yanzu, injiniya Abba Kabir Yusuf.
Abin lura a nan shine, a zaɓen 2023 da ya gabata, Gawuna shine ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a ƙarƙashin. Jagorancin tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yayin Abba shine ɗan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta NNPP ƙarƙashin jagorancin Kwankwaso. A yanzu an sauya hannu kenan; Gawuna ya koma gidan Kwankwaso, yayin da Abba ya koma gidan Ganduje.
A ɓangaren APC kuwa, rahotanni sun nuna cewa, an yi iyaka ƙoƙarin shawo kan Gawuna domin kada ya fice daga APC. Majiyoyi sun bayyana cewa, Fadar Shugaban ƙasa ta shiga tsakani, inda ta tura manyan jiga-jigan jam’iyya domin tattaunawa da shi.
Wani jigo a jam’iyyar ya bayyana cewa, “akwai matuƙar damuwa, domin ficewarsa na iya raunana tsarin jam’iyyar a Kano tare da kawo tangarɗa ga lissafin zaɓen 2027.”
Haka kuma ana zargin APC na duba yiwuwar ba shi tikitin takarar sanatan Kano ta Tsakiya kai tsaye, domin janyo hankalinsa ya zauna.
A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa, Gawuna ya yi tafiya zuwa Saudiyya domin yin umrah a watan Ramadan tare da kauce wa sadarwa daga masu tuntuɓar sa, don kada su kawo tangarɗa ga shirye-shiryensa na siyasa.
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa, idan wannan ƙawance tsakanin Gawuna da Kwankwaso ya kammala tabbata a mataki na takara, zai iya sauya fasalin siyasar Kano bakiɗaya. Wani masani, Aminu Bashir, ya bayyana wannan haɗaka a matsayin “mai sauya wasa”, yana mai cewa Gawuna na da karɓuwa a tsakanin matasa, malamai da ’yan kasuwa.
A ƙarshe, abin da ya bayyana a sarari shine cewa, ficewar Gawuna ba kawai murabus ba ne, illa wata alama ce ta sabbin ƙawance, ƙarin buri da kuma fara zafafan fafatawar siyasa gabanin zaɓen 2027 a Jihar Kano, wac ce ta saba ɗaukar hankalin siyasar ƙasa a koyaushe.
