“Jarumta ba ta da jinsi, kishin ƙasa ne ke bayyana ta”
Daga AISHA ASAS
A tarihi mata ba su da yawa da aka rubuta su da sunan jarumai da suka yi namijin ƙoƙari wurin fitar da al’umma daga wani ƙunci da suke ciki ta ƙarfin tuwo, masu kishin ƙasa da suka sadaukar da rayuwarsu don samar wa ƙasarsu damar walwala da ‘yanci.
Sai dai daga kaɗan da ake samun su a wannen fage sukan yi ƙoƙari na ban mamaki da har za a fara tunanin anya mace ce ta yi hakan. Wannan zai sa ba ɓata lokaci za su samu kansu a bakin duniya, yayin da za su shiga cikin tarihi. Ba kuwa don komai ba sai don irin jarumta da ƙarfin hali da suka nuna.
Shafin Gimbiya na wannan makon zai waiwaye ɗaya daga cikin manyan jaruman da Afirka take alfahari da su, kuma take cin moriyar jarumtarsu har kawo wa yau. Sakamakon irin ƙarfi da rashin tsoron da suka nuna don samar wa ‘yan baya damar kiran kansu masu ‘yanci.
Yaa Asantewaa, sarauniya mai daraja a ƙasar Ashanri wanda a yanzu aka sani da ƙasar Ghana, ta kasance mace ƙwaya ɗaya tilo da ta yi tsayin daka don kare martabar ƙasarta da mutuncin al’ummarta. Mace mai kamar maza da ta tabbatar da cewa jarumta ba daga jinsi ba ce, abu ne da zuciya ke ɗauka, kuma idan har mace za ta iya jure nauyinsa a zuciyarta, to tabbas za ta zama zakaran gwajin dafi a fagen daga.
Lokacin da Turawan Birtaniya suka ƙara damƙe ikon Ashanti, ba maza kaɗai suka tsaya ba, domin Yaa Ashatewaa tsaye ta yi a bakin daga, har ma tana ƙoƙarin kere mazan a dumfarar abokan daga masu barazana ga ‘yancin al’ummarta, wato turawan mulkin mallaka.
Yaa Asamtewaa ta ɗaga murya tana cewa, “Idan maza sun gaza, mu mata za mu tashi mu kare mutuncinmu.” Kuma ba ta gushe ba har sai da ta tabbatar da hakan a aikace, kuma duniya ta zama shaida. Wannan kalamai nata sun zama wani tambari da kuma kalaman tsuma zuciya da ƙwarin gwiwa ga matan Afrika.
Kafin mu yi nisa, shin wacce ce Ya Asantewaa?
An haifi Yaa Asantewa kusan shakara ta 1840, a cikin ƙasar Ashanti, a garin Ejisu. Ta fito ne daga babban gida, wanda a wancen lokacin hakan ke nufin gida mai ƙarfi a birnin, wato gidan sarauta.
A wannan ɓangare na duniya, al’ada ba ta yi wa mata shinge daga shugabanci ba, don haka mata na iya shugabantar al’umma ba tare da fuskantar wata matsala ba ta kasancewarsu mata ba.
Yaa Asentewaa ta taso cikin kulawa da kuma gata wanda ya dace da al’adar, duk da hakan ta kasance ta musamman a ɓangaren hikima da hangen nesa. Don tun tana ƙara aka shaida baiwar saurin fahimtar abubuwa da take da ita, da kuma warware matsaloli cikin hikima wanda ya girme shekarunta. Wannan ya sa ta zama ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarauta da aka haikanto matsayinsu tun kan su kai ga lokacin.
A lokacin da ta girma, ta samu matsayi babba na zama Uwar Sarauniya (ƙueen Mother) ta birnin Ejisu. Duk da cewa da yawa mun san wannnan matsayi a matsayin suna kawai ba tare da iko ba, kasancewar sa riƙo na sarauta daga rashin girman wanda aka naɗa a matsayin sarki ko kuma jiran mai hawa kujerar. Saidai abinda da yawan mutane ba su sani ba sarautar Uwar Sarauniya matsayi ne mai matuƙar muhimmanci, ba wai kawai alamar daraja ba ce.
ƙueen Mother na da ikon bada shawara ga sarki, wani lokacin har ma da yanke masa hukunci, da kuma jagorantar al’umma ta ɓangarori da dama, ciki har da yaƙi da difloasiyya.
Matsayinta ya bata damar fahimtar siyasa da al’amuran jama’a, wanda daga baya ya zama wani ginshiƙi da ya bata damar jagorantar babban yaƙi da Turawa.
Shin ya tsarin mulki da al’adu suke a Ashanti?
Ashanti tana da tsarin mulki mai ƙarfi da ya haɗa sarki, sarauniya (ba ɗaya baya) da kuma manyan shuwagabanni da ke da sunaye. A tasu al’ada wadda aka kira da Uwar Sarauniya ita ce mace shugaba da ke shugabantar wasu ɓangarori duk da cewa tana ƙarƙashin sarki ne. Saidai ita ce ke da alhakin jagorantar mata, da kula da al’amuran cikin gida da bayar da shawara a harkokin siyasa. Wannan tsarin ne ya ba wa Yaa Asantewaa damar yin tasiri sosai, musamman wajen jagorantar al’umma a lokutan rikici mai cike da ƙalubale.
Shin waɗanne irin nasarori Yaa Asantewa ta samu a tarihin mulkinta?
Babbar nasarar da Yaa Asantewa ta samu da duniya ta yi amo da shi shi ne, jagorancin Yaƙin Golden Stool, wanda aka fi sani da ‘War of the Golden Stool’.
Kalmar golden stool anan na ɗaukar ma’anar kujerar zinariya, wadda kuma ita ce alamar mulkin ƙasar Ashanti da irin haɗin kan al’ummarta.
Lokacin da Turawan Birtaniya suka nemi mallakar kujerar, Yaa Asantewaa ta yi yekuwa, ta yi kira ga al’umma da su tashi tsaye, kuma ta miƙe karan kanta, ta jagoranci dakarun ƙasar na daga mata da maza don ganin sun kare wannan alamar da ke bayyanasu a matsayin ƙasa.
Baya ga haka, ta kasance jagorar yaƙi mace, abinda ba a saba gani ba a tarihin Afrika. Ta horar da mayaƙa maza da mata tare da koyar da su dabarun yaƙi. Wanda wannan ya sa ta bayyana a aikace cewa mata fa na daga gudunmuwar da za su iya bayarwa a fagen yaƙi da kuma harkar siyasa, ba wai sun tsaya a iya hidimar gida ba.
A lokacin yaƙi Yaa Asantewa ta shimfiɗa shiri mai kyau tun daga dabarun kare garuruwa, kafa matsugunan mayaƙa, da kuma amfani da hikima wurin shige da ficen mayaƙanta. Wanda wannan na daga cikin dalilan da ya sa mayaƙanta suka nuna banjinta da ta matuƙar bayar da mamaki. Hakan kuwa ya biyo bayan irin bin umurninta da suka yi tamkar yadda suke bin na sarki.
Haka muka Yaa Asantewa ta kasance mace ɗaya tilo da aka rubuta sunanta a matsayin jagora a yaƙi kai tsaye a Afrika a ƙarni na 19. Sunanta ya shiga a tarihi a matsayin alamar juriya, kishin ƙasa, da kuma ƙarfin zuciya.
Tarihinta ya zama wani babban darasi ga matasa da mata har kawowa yanzu, musamman masu tambaba kan yiwar mace ta iya jagoranci ko akasin haka.
Ko akwai ƙalubalen da ta fuskata?
Nasara irin wadda Yaa Asantewaa ta samu kawai zata tabbatar maka da tabbas akwai ƙalubale a tafiyar kafin a tarar da nasarar. Kuma za ku iya amincewa idan na ce ƙalubalen bai zo mata da sauƙi ba, domin masu azancin zance suna cewa, idan ka ji wane to ba banza ba, domin ko ba a sha dare ba, an sha rana.
Abu na farko da ta fuskanata akwai kasancewarta mace, duk da cewa al’umma ta aminta da jagorancin mace a lokacin hakan bai hana wasu ganin rashin dacewar jagorancinta a matsayinta ta mace, don haka ta haɗu da ƙalubale na bijirewar wani ɓangare na al’ummarta wanda hakan ya haifar da matsaloli da dama.
Yaƙin da ta yi ya haifar da hasarar dukiya da ƙalubalen tattalin arziki wanda ta fuskanta a matsayinta ta jagorar al’umma.
Turawan Birtaniya sun kama Yaa Asantewaa tare da wasu shuwagabanni kafin a kaita gudun hijira zuwa Seychelles. Duk da wannan abu da aka yi mata, bai sa ƙafafuwanta suka sare ba, domin ta kasance tana jagorantar mutanenta daga nesa.
Ta kula da mata da yara, kuma tana mai aiken shawarwari ga shuwagabanni, sannan ta riƙe darajar Ashanti a matsayin rayuwarta.
Mene ne tasirin rayuwarta ga mata?
Yaa Asantewaa ta sauya tunanin mutane game da mata a Afirka:
Ta nuna cewa mace na iya jagoranci cikin manyan harkoki, har ma a yaƙi.
Ta ƙarfafa mata su daina jin tsoron tsayawa kan gaskiya da kare haƙƙinsu.
Ta zama abin koyi ga mata masu son shiga siyasa, shugabanci, da fafutukar ‘yanci.
Har yau, ana koyar da tarihi da jarumtarta a makarantu da cibiyoyin al’adu a Ghana da Afirka baki ɗaya.
Daga cikin fitattun kalaman da ake yawan tuna Yaa Asantewaa da su akwai:
“Idan mazan Ashanti ba za su yi yaƙi ba, mu mata za mu yi. Za mu yi yaƙi har sai na ƙarshe daga cikinmu.”
“Jarumta ba ta da jinsi, kishin ƙasa ne ke bayyana ta.”
“ƙarfi da juriya sun fi duk wani makami.”
Labarin Yaa Asantewaa ba kawai labarin mace da ta yi abin faɗa ba ne, darasi ne na ƙarfin hali, kishin ƙasa, da jajircewa. Ta tabbatar da cewa, mace ba tilas sai ta tsaya a gefe ba; tana iya jagoranci, kare al’umma, kuma ta rubuta tarihi.
Ga kowacce mace da ke fuskantar ƙalubale, ki sani, kina da wani ajiyayen ƙarfi a tare da ke, sai kin yarda da kanki, kuma kin tashi tsaye ne za ki gan shi a zahiri.
