Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya kai ziyarar gani da ido a garin Sayaya a ƙaramar hukumar Matazu inda ‘yan bindiga suka shiga da rana suka kashe ɗan sanda da ƙone asibitin shan magani tare da fasa shaguna inda suka kwashe duk abinda suka samu.
Malam Dikko Raɗɗa ya ziyarci wuraren da yan ta’addan suka lalata domin gane wa idanun sa.
Daga nan gwamnan yayi wa shugaban ‘yan sanda na ƙaramar hukumar ta’aziyar rasuwar ɗan sanda da ‘yan bindiga suka kashe,ya sadu da al’ummar Sayaya inda ya jajanta masu.
Ya umurci a ƙara kai jami’an tsaro a garin domin ƙarfafa tsaro a garin na Sayaya da ke ƙaramar hukumar.
A baya bayan nan ‘yan bindigan suka shiga wasu unguwanni a cikin garin Funtua bayan sallar magrib inda suka raunata wasu mutane tare da awon gaba da shanu da dama.
