Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar adawa ta ADC a jihar Katsina ta shirya gudanar da zaɓen sabbin shugabannin jam’iyar a matakin gunduma,mazaɓu, ƙananan hukumomi da jiha.
Alhaji Tukur Lawal Ɓatagarawa ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce uwar jam’iyyar ta ƙasa ta bada umurnin gudanar da zaɓen duk da umurnin hukumar zaɓe ta Kasa da rusa shugabancin jam’iyyar.
Ya ce bayyana umurnin hukumar zaɓe ta ƙasa a matsayin zalunci da munafurci tare da wata munakitsa ta ƙarƙashin ƙasa domin a hana jam’iyar su shiga zaɓe.
Ɓatagarawa wanda tsohon ƙaramin ministan Ilimi a mulkin Obasanjo ya ce za su cigaba da shirye shirye na gudanar da babban taron jam’iyyar ta ƙasa inda za su zaɓi sabbin shugabanni na ƙasa duk da umurnin INEC.
Ya kuma bayyana shirin hukumar zaɓe ta ƙasa na sake sabunta katin zaɓe cikin kwanaki 31 a matsayin zalunci da wata ɓoyayyar shiri na hana jam’iyar su ta ADC galaba a zaɓe mai zuwa.
Lawal Batagarawa ya sanar da cewa yanzu haka lauyoyi na jam’iyar sun fara shirye-shirye kai hukumar kotu.
Ya yi ta’aziya da jaje ga al’ummar Musawa, Matazu,Sayaya da wasu garuruwa a jihar Katsina da a baya bayan nan yan bindiga suka hallaka mutane da dama tare da rasa dukiya a yankunan.
Ɓatagarawa ya zargi gwamnatin tarayya da rashin taɓuka komai wajan ƙare rayuka da dukiyar al’umma na wasu jihohin Arewacin ƙasar.
