ADC ta musanta jita-jitar murabus, ta ce David Mark na ƙoƙarin kai ta ga nasara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Shugabanta na Ƙasa na tsagi, Sanata David Mark ya sauka daga mukaminsa, tana mai bayyana su a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.

A wata sanarwa da Ofishin Yaɗa Labarai na Shugaban Jam’iyyar ya fitar, ADC ta bayyana jita-jitar a matsayin ƙage mai muni da masu yaɗa farfaganda marasa hankali, raunana, kuma marasa tunani suka ƙago.

Sanarwar ta tabbatar da cewa Sanata David Mark na nan daram a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na Kasa, tare da jaddada cewa babu wani shiri ko tunanin murabus daga gare shi ko shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa shugabancinta a haɗe yake, kuma yana mai da hankali wajen ƙarfafa dimukraɗiyya da samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Nijeriya.

Kazalika, ta yi gargadi akan duk wani yunƙuri na tayar da zaune tsaye a cikin jam’iyyar abu ne da ake yi saboda fargabar tasirin ADC da ke ƙaruwa da kuma shirye-shiryen siyasa da ke tafe gabanin zaɓen 2027, tan mai kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da waɗannan jita-jita.

By Babaji