Yanzu-yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi, Usman Ankwai ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kakakin Majalisar Dokoki a Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Usman Ankwai ya rasu.

Tuni dai ‘yan uwa da abokan arziƙi daga takwarori da ‘yan siyasa suka riƙa miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin a jihar.

Ankwai shi ne kakaki a majalisar dokokin jihar ta 10, kuma yana wakiltar mazaɓar Zuru.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san a wani hali yake ba gabanin rasuwar ba.

By Babaji