
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce zargin da wani tsohon soja da aka kora mai suna Rotimi Olamilekan ya yi na cewa sojoji na sayen kayan aiki da kansu ciki har da rigunan aiki, hulunan kariya da rigunan kariya ba gaskiya ba ne.
Da take martani akan zargi wanda aka yaɗa a kafafen sada zumunta da na labarai, rundunar ta ce tana ba da muhimmanci sosai ga jin daɗi, tsaro da kariyar jami’anta a kodayaushe.
A wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’ar rundunar ta riƙo, Kanal Appolonia Anele, ta fitar a ranar Talata, rundunar ta jaddada cewa samar da kayan aiki kamar su riguna, kayan aiki, makamai, harsasai da sauran kayan aikin soja, nauyi ne akan hukumar da ake aiwatarwa ta hanyar tsarin tanadi da rarrabawa da doka ta tanada.
“Rundunonin ajiyar kayan soja na musamman ne ke kula da saye, ajiya da kuma rarraba waɗannan kayayyaki domin tabbatar da cewa sojoji suna da isassun kayan aiki don gudanar da ayyukansu”, kamar yadda sanarwar ta fitar.
Kasancewar wasu jami’ai na iya ƙara wasu kayan bisa raɗin kansu don jin daɗi, hakan ba yana nufin akwai wata matsala a tsarin, wanda dokar ƙasa da ta aikin soja suka tanada.
“Zargin cewa sojoji na aiki ba tare da kayan kariya ba ba gaskiya ba ne, kuma yana da haɗari domin yana rage amincewar jama’a da kuma ƙarfafa gwiwar sojoji”, inji sanarwar.
