
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’ar Jos da Rundunar Sojin Nijeriya sun yi watsi da rahoton ƙarya da ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya da ke zargin cewa ana rikici a farfajiyar jami’ar, inda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin yaɗa abin da zai firgita al’umma.
Rahoton, wanda aka baza da ke ɗauke da yanayin ɓarkewar rikici a jami’ar, ya yi ikirarin cewa ƙuncin da ɗalibai suke ciki ya rikiɗa ya zama tashin-tashina.
Wani bincike daga THE STAR da tabbatarwa daga hukumomin jami’ar sun nuna cewa babu wani rikici da ke faruwa a jami’ar, inda hasali ma ana cigaba da gudanar da harkoki yadda aka saba.
Hukumomin sun kuma ce hotunan da ake watsawa tare da rahoton, ba na gaskiya ba ne, ƙirƙira ce ta fasahar AI, wadda ba ta da alaƙa da kowane irin al’amari na zahiri a jami’ar.
Akan haka ne babban jami’in sojin atisayen ENDURING PEACE a Jihar Filato, Manjo-Janar E.F. Oyinlola ya jagoranci sojoji zuwa jami’ar don gane wa idonsa sakamakon bazuwar rahoton ƙaryar.
