Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina ta gudanar da karatu na biyu kan ƙudirin dokar da ke da nufin kafa hukumar kula da makarantun sakandiren gwamnati (Katsina State Secondary School Management Board) a jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai, shi ne ya gabatar da ƙudirin, inda ya bayyana cewa Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ne ya nemi a samar da wannan doka domin ƙarfafa tsarin tafiyar da makarantun sakandire a faɗin jihar.
A cewarsa, idan aka amince da dokar, za ta taimaka wajen tsara yadda ake gudanar da harkokin makarantu, kula da ayyukansu, da kuma inganta ilimi a matakin sakandire domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai.
Bayan tattaunawa mai zurfi da yan majalisar suka yi, an miƙa ƙudirin dokar zuwa kwamitin ilimi na majalisar, domin yin cikakken nazari tare da gabatar da rahoto kan tasirin dokar ga ci gaban ilimi a jihar.
Haka zalika majalisar tayi kira kan gyaran gadar Tsabawa a Batsari.
A wani ɓangare kuma, majalisar ta yi kira ga ɓangaren zartaswa da ya ɗauki matakin gaggawa wajen sake gina gadar Tsabawa da ke mazaɓar Abadau-Kagara a ƙaramar hukumar Batsari.
Ɗan majalisa mai wakiltar Batsari, Hon. Mustapha Tukur Ruma, ya gabatar da ƙudirin haka, inda ya bayyana cewa gadar na da matuƙar muhimmanci wajen haɗa ƙananan hukumomin Batsari da Kurfi.
Ya ƙara da cewa lalacewar gadar na kawo cikas ga rayuwar al’umma, musamman manoma da ke gudanar da noman rani da damina a yankin.
Mambobin majalisar sun amince da ƙudirin, inda Kakakin Majalisar, Rt. Honourable Nasir Yahaya Daura, ya bayar da umarnin tura shi ga ɓangaren zartaswa domin ɗaukar matakin da ya dace.
