Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Aƙalla matasa 2000 za’a ɗauka matsayin sabbin jami’an yan sanda a Katsina a cewar Hon. Yau Ahmad Nowa Dandume,mai ba gwamna shawara kan samar da aikin yi, ya faɗi haka a ziyarar da yakai wajen tantance jami’an yan sandan da za a ɗauka a Katsina.
‘Yan sandan Najeriya (Police Constables) dubu 50,000 gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya ɗauka a bana.
Mai bai wa shawara kan samar da ayyukan yi ga Matasa, Hon. Yau Ahmad Nowa Dandume, yana cigaba da kai ziyara wurin da ake gudanar da tantancewar domin duba yadda ake tafiyar da aikin. A Police Officers’ Mess da ke GRA cikin birnin Katsina, inda ake gudanar da shirin Physical and Credential Screening 2026 ga matasan ‘yan asalin jihar da suka kammala rajistar neman aikin ta yanar gizo.
Shirin ɗaukar sabbin jami’an ‘yan sanda 50,000 na gudana ne ƙarƙashin hukumar Kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF).
An tsara gudanar da wannan tantancewa inda ake duba lafiyar jiki da kuma ingancin takardun masu neman aikin.
Takardun da masu neman aikin suka dace su buga daga shafin rajista. An buƙaci dukkan masu neman aikin da su shiga shafin rajista na npfapplication.psc.gov.ng domin duba matsayinsu tare da buga wadannan takardu kafin ranar da aka gaiyace su.
Bugu da ƙari akwai abubuwan da dole a gabatar lokacin tantancewa. Masu neman aikin za su gabatar da wadannan takardu:
Hakazalika, an umarci masu neman aikin su halarci wurin tantancewar a ranar da aka ware musu, suna sanye da takalman canvas fari, riga fari (T-shirt), wando gajere fari (short), da safar ƙafa fara (white stockings).
