
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yanayi na ci-gaban siyasa a Jihar Kano, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon sanata, Kabiru Gaya ya fice daga jam’iyyar APC a hukumance.
Gaya, wanda ya riƙe muƙamin sanatan Kano ta Kudu, ya sanar da matakin nasa na barin jam’iyyar ne a wata wasiƙa zuwa ga shugaban yankinsa na Gaya ta Arewa a Ƙaramar Hukumar Gaya ta Jihar Kano.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa shawarwari daga ‘yan mazaɓarsa da kuma ganin dacewar hakan daga gare shi na ya bar jam’iyyar.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damarmaki da goyon baya da ta ba shi a ƙarƙashinta na riƙe muƙamin sanata daga 2015 zuwa 2023.
Barin APC da jigon siyasar Kanon ya yi, ya nuna wani gagarumin sauyi a harkokin siyasar jihar musamman duba da yadda ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.
