Daga JOHN D. WADA a Keffi
Shugaban ƙungiyar mabiya addinin Kirista na ƙasa CAN reshin ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa Rev. Dr. Kefas Musa ya shawarci kiristoci a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su riƙa bincikan kansu don su ga inda matsayinsu yake a bautar ubangiji.
Rev. Dr. Kefas Musa ya bada shawarar ne a lokacin da yake gabatar da wa’azinsa a wajen wani babban bikin Easter wanda ƙungiyar CAN ɗin na ƙaramar hukumar Keffi ta shirya ta gabatar a cocin Katolika na St. James da ke birnin Keffi ranar Litinin na mako da ake ciki.
Yace kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da mahimmancin mabiyin Annabi Isa Almasihu ya riƙa bincikan kansa akai-akai don ya nemi gafarar Allah a duk inda ya yi kuskure kafin ya yi dana-sani daga bisani.
Wa’azin nasa mai taken ‘muhimmancin ikon tashuwar matattu’ ya kuma ƙalubalanci kiristoci su tabbatar suna jurewa a duk lokacin da suka samu kansu a cikin wasu ƙalubalai na rayuwa.
Rev. Dr. Kefas Musa ya kuma buƙace su cewa su rika yin addu’a a koyaushe don samun ikon bincikan kansu yadda ya dace ba su riƙa dogara ga ƙarfin su ba.
Har ila yau shugaban ƙungiyar kiristoci ta CAN reshin ƙaramar hukumar Keffi, Rev. Dr. Kefas Musa ya bayyana ire-iren wahalhalu da Annabi Isa Almasihu ya sha akan giciye inda yace a lokacin da ya samu damar ziyartar ƙasa mai tsarki ta Jerusalem ya gane wa idanunsa wuraren tarihin da hakan a cewarsa ya tabbatar da gaskiyar duka labarin litafi mai tsarki Bibul game da mutuwa da tashin Annabi Isa kana yayi kira ga mabiya addinin Kirista baki ɗaya suyi rayuwa cikin tsorion Allah.
Daganan sai Rev. Kefas ya kuma yi amfani da damar inda ya bukaci mambobin CAN a ƙaramar hukumar su tabbatar sun yi rajistar katin kaɗa ƙuri’un su, kuma su fito ƙwansu da kwarkwata don a fafata da su a duka zaɓuka dake tafe a jihar.
A yayin taron Easter ɗin na musamman da CAN na ƙaramar hukumar Keffi ɗin ta shirya an gudanar da waƙoƙin yabon Ubangiji daga ƙungiyoyin mujami’ai daban-daban tare da gabatar da wasan kwaikwayo da sauransu.
