Ɗan Sarkin Daura ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar ɗan majalisar wakilai

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Muhammad Ɗaha Umar Faruk, babban ɗan Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya ta Ɓaure/Zango a babban zaɓen 2027.

Faruk, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Ɗanburam Daura, ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara don amsa kiraye-kirayen da jama’a ke yi masa na neman ya wakilce su a majalisar tarayya.

“Ina so in sanar da dukkan magoya bayana cewa ni, Muhammad Ɗaha Faruk, na yanke shawarar amsa kiransu,” in ji shi.

“Na amince na tsaya takarar kujerar majalisar tarayya don wakiltar mazaɓar tarayya ta Ɓaure/Zango a zaɓen 2027.”

Matashin basaraken ya kuma gargaɗi mabiyansa game da yaƙin neman zaɓe mai cutarwa, yana mai kira gare su da su ci gaba da nuna ɗabi’a a duk lokacin da zaɓe ya ƙarato.

“Ina so in yi amfani da wannan damar don yin kira ga dukkan magoya bayana da su guji duk wani aiki da zai iya zama izgili ko rashin girmama kowa da sunan goyon bayana,” in ji shi.

Duk da cewa Faruk bai bayyana takamaiman jam’iyyar da yake son tsayawa takara a kai ba, masu lura da al’amura da dama sun bayyana cewa rashin bayyana jam’iyyar da zai tsaya takara wani salo ne na dabarun yin takara.

Sai dai majiyoyi, da ke kusa da ɗan takarar sun nuna cewa ɗan gidan sarkin na Daura zai iya tsayawa takara ko dai a jam’iyyar APC ko kuma ADC.

By ukarofi