Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kusan makonni biyu bayan Ministan Wutar Lantarki na ƙasa, Adebayo Adelabu, ya yi wa ’yan Nijeriya alƙawarin dawo da ingantacciyar wutar lantarki, har yanzu tsarin lantarki na ƙasa bai kai matakin da ake buƙata ba, lamarin da ke ƙara jefa jama’a cikin damuwa da ƙunci sakamakon yawaitar katsewar wuta.
A lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, ministan ya nemi afuwar ’yan ƙasa kan matsalolin wutar lantarki da ya bayyana a matsayin na wucin gadi, inda ya danganta su da ƙarancin iskar gas da kuma gyaran bututun mai.
Ya kuma yi alƙawarin cewa za a ga sauyi cikin makonni biyu, sai dai wannan wa’adin ya cika ba tare da an samu gagarumin ci gaba ba.
Bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa yawan wutar lantarkin da ake samarwa a ƙasar na zagayawa ne tsakanin megawatt 3,000 zuwa 4,000, ƙasa da matakin sama da megawatt 5,000 da aka riƙa samu a shekarar 2025.
A ranar Laraba da safe, kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 a ƙasar sun raba kimanin megawatt 3,500 kacal—abin da ya zan fi na baya amma har yanzu bai wadatar ba.
Bincike ya nuna cewa matsalar ba wai ƙarancin gas kaɗai ba ce ke haddasa koma bayan ba, har ma da basussukan da ake bin kamfanonin samar da wuta, wanda ya sa masu samar da gas ke barazanar dakatar da isar da shi. Haka kuma, kamfanonin rarraba wuta na fuskantar zargi kan ƙin karɓar wutar da ake samarwa, abin da ke jefa tsarin cikin tangarɗa.
Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wuta, Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wuta na ƙin karɓar wutar da ake samarwa, lamarin da ke tilasta wa masu sarrafa tsarin rage yawan wutar da ake fitarwa.
Ta ƙara da cewa, a watan Janairu, an samar da matsakaicin megawatt 4,541, amma fiye da megawatt 2,900 sun tafi a banza ba tare da amfani ba. A watan Fabrairu kuwa, an samar da megawatt 4,218, inda fiye da megawatt 3,200 ba a karɓe su ba. Duk da cewa tashoshin wutar lantarki 30 na ƙasar na da ƙarfin samar da megawatt 15,500, amma a zahiri ba a iya samar da fiye da megawatt 7,000 saboda matsalolin kuɗi, yayin da tsarin watsawa da rarraba wuta ke iya ɗaukar megawatt 4,000 zuwa 4,500 kawai.
Sai dai kamfanonin rarraba wuta sun musanta zargin ƙin karɓar wutar da gangan, suna mai cewa matsalolin tsarin watsawa ne ke hana su karɓar wasu kayayyakin wutar da ba za su iya rarrabawa yadda ya kamata ba.
A nata ɓangaren, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nujeriya ya ce yana da ƙarfin raba megawatt 8,700, yana mai ƙaryata wasu rahotanni da ke nuna ƙarancin ƙarfinsa.
Yayin da ake ci gaba da cacar baki tsakanin ɓangarorin da ke cikin harkar lantarki, al’ummar Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsanancin katsewar wuta, ba tare da tabbacin lokacin da za a samu daidaito ba kamar yadda aka yi alƙawari.
