Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB), ta buƙaci iyaye da ɗalibai da su riƙa ɗaga murya idan suna da tabbacin makinsu na jarrabawar UTME amma aka hana su samun gurbin karatu a makarantun da suka zaɓa.
Magatakardar JAMB, Ishaƙ Oloyede, ne ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin “Good Morning Nigeria” na gidan talbijin na NTA, inda ya jaddada cewa tsarin ɗaukar ɗalibai a yanzu ya fi zama a sarari kuma yana bai wa kowa dama daidai.
Ya bayyana cewa duk da ci gaban da aka samu, wasu iyaye na ci gaba da neman hanyoyin da ba su dace ba wajen neman gurbin karatu ga ’ya’yansu, saboda sun saba da irin waɗannan hanyoyi kuma suna ganin babu wata mafita a waje da hakan.
A cewarsa, sau da dama iyaye kan tuntuɓe shi domin neman taimako, amma ya kan ƙi tsoma baki, duk da haka sai ga shi ɗaliban suna samun gurbin karatu ba tare da wata matsala ba. Wannan, a cewarsa, shaida ce cewa tsarin ya riga ya zama mai gaskiya kuma ba ya buƙatar wata tsoma baki daga waje.
Oloyede ya jaddada cewa tsarin tantancewa da bayar da guraben karatu na JAMB, musamman ta hanyar CAPS, ya kawo sauyi mai girma, inda ya rage zargin maguɗi tare da tabbatar da gaskiya da adalci ga dukkan masu neman shiga jami’a.
Ya ce, idan ɗalibi yana da ƙwarin gwiwa kan makinsa kuma ya cancanci samun gurbin karatu amma aka hana shi, to ya kamata ya kai ƙorafi kai tsaye ga JAMB domin a bincika lamarin.
Dangane da shigar kai tsaye, wato Direct Entry, Oloyede ya bayyana cewa hukumar ta ƙara tsaurara matakan tantance takardu, lamarin da ya sa ya zama da wuya a yi amfani da takardun bogi. Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2023, an samu raguwar masu neman shiga ta wannan hanya saboda tsauraran matakan bincike.
Haka kuma, ya ce JAMB na aiki tare da cibiyoyi daban-daban, ciki har da jami’o’in ƙasashen waje, domin tabbatar da sahihancin takardun da ake gabatarwa, inda a wannan shekara ma an gano wasu takardun digiri da aka gabatar ba su da tushe daga makarantu da aka ambata.
A ƙarshe, ya bayyana cewa irin waɗannan matsaloli a baya sun faru ne saboda ba a haɗa duba takardun A-leɓel cikin aikin JAMB kai tsaye ba, amma yanzu an gyara wannan gibi ta hanyar haɗin gwiwa da masana daga sashen jami’o’i domin ƙarfafa sahihancin tsarin.
