Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC), ta sanar da cewa umarninta na tilasta wa kamfanonin sadarwa su biya diyya ga masu amfani da layukansu saboda rashin ingancin sabis zai fara aiki daga wannan watan na Afrilu 2026.
A cikin wata takardar tambayoyi da amsoshi (FAƙ) da hukumar ta fitar a ranar Talata, NCC ta bayyana yadda tsarin biyan diyya zai gudana da kuma irin masu amfani da za su cancanci amfana da shi.
Hukumar ta ce, wannan sabon tsari ya shafi kamfanonin sadarwa na wayar hannu (Mobile Network Operators) da suka gaza cika ƙa’idojin da aka gindaya na ingancin sabis (Key Performance Indicators for ƙuality of Serɓice).
Daga cikin manyan kamfanonin da abin ya shafa akwai MTN, Airtel, Globacom da 9mobile, duk da cewa hukumar ba ta fayyace takamaiman kamfanonin da suka karya ƙa’idojin ba.
NCC ta kuma bayyana cewa akwai wani tsarin daban da aka tanada tun farko domin masu samar da intanet, wanda ke aiki daban da wannan sabon tsarin.
A ƙarƙashin sabon umarnin, za a riƙa biyan diyya ne idan aka samu matsaloli a sabis na kira (ɓoice calls), intanet (data), da saƙonnin SMS. Don samun wannan diyya, dole ne mai amfani ya fuskanci matsalar sadarwa a wani yanki na ƙaramar hukuma da abin ya shafa, sannan kuma ya yi akalla wata mu’amala da ke haifar da kuɗin shiga kamar yin kira mai caji, aika SMS ko amfani da data a lokacin da matsalar ta faru.
Hukumar ta ƙara da cewa, wannan dama ta shafi dukkan masu amfani, ko na kashin kai ko kuma kamfanoni.
Abu mafi muhimmanci shi ne, NCC ta jaddada cewa ba sai masu amfani sun nemi diyya ba. Kamfanonin sadarwa ne aka ɗora wa alhakin gano wadanda abin ya shafa da kuma biyan su diyya kai tsaye.
Hukumar ta ce wannan tsari ba zai maye gurbin dokokin kariyar masu amfani ba, sai dai zai ƙara wani sabon mataki na kai tsaye wajen tabbatar da an biya masu amfani haƙƙinsu, bisa tanade-tanaden dokoki irin su Consumer Code of Practice Regulations 2024 da ƙuality of Serɓice Regulations 2024.
Sai dai NCC ta yi gargaɗi cewa ba duk wata matsalar sadarwa ba ce za ta kai ga biyan diyya, domin ƙananan matsaloli ko waɗanda aka warware cikin gaggawa ba za su kai matakin da ake buƙata ba.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke yi na inganta ayyukan kamfanonin sadarwa tare da tabbatar da cewa suna bin ƙa’idoji tare da ba wa ‘yan Nijeriya sabis mai inganci a duk faɗin ƙasar.
