Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bunƙasa yaƙi da rashin tsaro, musamman a yankunan da a baya suka fuskanci matsalar ‘yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake karɓar baƙuncin sabon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 14, Bello Shehu, wanda tsohon kwamishinan ‘yan sanda da kuma wanda ya maye gurbinsa, CP Umar Fagge a fadar gwamnatin jihar.
CP Umar Fagge na da sama da shekaru 30 yana aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya, inda ya samu ƙwarewa sosai a fannoni daban-daban kamar gudanar da ayyuka, bincike, da kuma harkokin gudanarwa a jihohi da dama ciki har da Sokoto, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina da Legas.
Ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a sassa daban-daban da kuma ƙungiyoyin musamman na rundunar, sannan ya taɓa zama mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da kuɗi da gudanarwa.
Ya yi aiki a matsayin mataimakin kwamanda a kwalejin ‘yan sanda da ke Ikeja, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen horas da jami’an ƙasa da inganta ƙwarewarsu.
CP Fagge ya kuma halarci manyan kwasa-kwasan ƙwarewa ciki har da na jagoranci da tsare-tsare (Strategic Leadership and Command Course) a kwalejin ma’aikatan ‘yan sanda da ke Jos.
A jawabin maraba,Gwamna Raɗɗa ya yaba wa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa ci gaba da tallafa wa jihar, tare da taya tsohon kwamishinan ‘yan sanda murna bisa ɗaukaka da aka yi masa zuwa mukamin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, yana mai cewa ya cancanci hakan.
Gwamnan ya bayyana cewa yanayin tsaro a jihar Katsina ya samu gagarumin ci gaba, inda wasu ƙananan hukumomi da ke kan gaba a matsalar tsaro yanzu suka fara samun kwanciyar hankali.
Ya ce yankunan da a baya ake kallon su masu haɗari yanzu suna samun zaman lafiya a hankali, sakamakon haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro da kuma al’umma.
Ya ce: “Mun ga ingantuwar tsaro a wurare da dama da a baya suke cikin rikici. Hukumomin tsaronmu tare da haɗin gwiwar al’umma sun samu nasarori masu yawa wajen dawo da zaman lafiya.”
Gwamna Raɗɗa ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin kai tsakanin dukkan hukumomin tsaro da kuma tsare-tsaren al’umma wajen magance sabbin barazanar tsaro.
Ya kuma bayyana cewa kafa rundunar Katsina State Community Watch Corps ta taimaka matuƙa wajen tattara bayanan sirri da kuma saurin ɗaukar mataki a matakin al’umma.
Ya ƙara da cewa: “Tsaro alhakin kowa ne. Rundunar Community Watch Corps ta kawo gagarumin sauyi saboda sun san yankunansu kuma suna bayar da bayanai cikin lokaci.”
Gwamnan ya tabbatar wa sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda cikakken goyon bayan gwamnatin jihar da kuma samar da kayan aiki domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin jihar.
A nasa jawabin, mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 14, Bello Shehu, ya yabawa shugabancin Gwamna Raɗɗa da sauye-sauyen tsaro da ya kawo, yana mai cewa su ne suka taimaka wajen samun nasarorin da ake gani a jihar.
Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda ya nuna godiya bisa goyon bayan da aka ba shi a lokacin aikinsa, tare da bayyana ƙwarin gwiwarsa ga wanda ya gaje shi na ci gaba da inganta nasarorin da aka samu.
Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Umar Fagge, ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, tare da mai da hankali kan aikin ‘yan sanda bisa bayanan sirri, ayyukan rigakafi, da kuma hulɗa da al’umma domin rage aikata laifuka.
Ya tabbatar da cewa rundunar da yake jagoranta za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Katsina.
Ana sa ran CP Umar Fagge zai ƙara ƙarfafa tsarin aikin ‘yan sanda a jihar tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin ɗorewar zaman lafiya da tsaro.
