Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya hannu kan wata doka ta musamman da ke da nufin daƙile matsalar ƙauraye da yan bangar siyasa faɗin jihar.
An sanya wa dokar, mai taken Katsina State Kauraye Activities and Operations Order 2026, hannu a gidan gwamnati da ke Katsina, a gaban manyan jami’an tsaro da hukumomin gwamnati da abin ya shafa.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙaruwa da ake samu na ayyukan da suka saɓa wa doka, musamman a cikin birnin Katsina.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido ta bari rashin tsaro da aikata laifuka su ci gaba ba. Ya kuma ce kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
A matsayin wani ɓangare na sabbin matakan, gwamnan ya amince da kafa kwamiti na musamman na aiki wanda ya ƙunshi jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya, DSS, NSCDC, NDLEA, Community Watch Corps, hukumar Hisbah, ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ma’aikatar shari’a, ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, da kuma ALGON.
An ɗora wa kwamitin alhakin gano da rushe ƙungiyoyin masu aikata laifi, gudanar da ayyukan sirri na tsaro, kama waɗanda ake zargi, ƙwace makamai da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen aikata laifi, sa ido kan wuraren da ake yawan aikata laifi, da tabbatar da gurfanar da masu laifi a gaban kotun tafi da gidanka.
Gwamnan ya ce zai yi aiki tare da shugabannin al’umma, sarakuna, da malamai domin hana ɗaukar matasa cikin irin waɗannan ƙungiyoyi.
Dikko Raɗɗa ya kuma sanar da kafa kotun tafi-da-gidanka domin tabbatar da gaggauta shari’ar masu laifi. Sannan ya sanar da cewa duk wanda yazo neman belin waɗanda aka kama da wannan laifuka to shima doka za ta ɗauki mataki kanshi.
Wannan shiri zai gudana ne haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar Shari’a da Ofishin babban alƙalin Jihar Katsina.
Ya ƙara da cewa wannan Dokar na daga cikin manyan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin dawo da zaman lafiya, ƙarfafa tsaron cikin gida, da samar da ingantaccen yanayi ga dukkan al’ummar Jihar Katsina.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da sakataren gwamnati, Barr. Abdullahi Garba Faskari, PPS, Alh Abdullahi Aliyu Turaji, Kwamishinan Harkokin Tsaro, Kwamishinan Harkokin Shari’ah, Shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon Isah Miqdad, wakilin kwamishinan yan Sanda da sauransu.
