ADC ta yi wa kundin dokokinta gyara yayin da ta kammala babban taronta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Talata Jam’iyyar ADC ta kammala babban taronta a Abuja, inda daliget suka gudanar da zaɓen yi wa kundin dokokin jam’iyyar kwaskwarima.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan kammala zaɓen, Shugaban kwamitin zaɓen kuma tsohon Gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha ya sanar da sakamakonsa.

Ya ce, deliget guda 1,576 ne aka tantance yayin da aka samu lalatattun ƙuri’a guda 11. Jimillar deliget
1,471 ne suka yi zaɓen amincewa da yi wa dokokin ADC gyaran fuska, wanda hakan ke wakiltar kaso 94.

A zaman majalisar zartarwar jam’iyyar (NEC) na 99, ADC ta sauke kwamitin ayyuka (NWC) ƙarƙashin jagorancin Cif Ralph Nwosu, yayin da na su David Mark ya karɓi ragamar jagorancin jam’iyyar.

Da yake jawabin rufe taron, Shugaban jam’iyyar, Sanata David Mark ya bayyana cewa bai taɓa halartar irin taron ba a zamansa na jam’iyyar PDP ganin yadda ya samu tsari mai kyau acikinsa, wanda hakan ke nuna jam’iyyar ta shirya tsaf wajen tunkarar 2027.

By Babaji