Injiniya Muttaƙa Rabe ya bayyana aniyar tsayawa takarar sanatan Katsina

Spread the love

Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sanata mai wakiltar shiyyar Katsina a Majalisar Dattawan Tarayyar Nijeriya.

Darma ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai, inda ya ce matakin da ya ɗauka ya biyo bayan kiraye-kirayen da ya ce ya samu daga al’umma, musamman daga yankin da ke da ƙananan hukumomi 11.

Injiniya Muttaƙa ya ce lamarin ya ƙara ɗaukar sabon salo ne a daren da ya gabata, lokacin da wasu mutane kimanin 50 suka ziyarce shi a gidansa, inda suka matsa masa lamba kan ya bayyana matsayinsa kan batun takarar.

“Na nemi lokaci domin in tuntuɓi abokaina, abokan aiki, ƙwararru da kuma masu ba ni shawara a harkar siyasa. Amma zuwan da suka yi ya sa dole na bayyana matsayina kai tsaye,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa da a ce an nemi ya tsaya wata takara da ba ta dace da abin da ya yi amanna da shi ba, da ya ƙi amincewa, sai dai ya ce wannan takara ta dace da ƙwarewarsa da kuma abin da ya yi amanna din da shi, lamarin da ya sa ya amince.

Ya jaddada cewa ba ya ganin ya fi sauran masu neman takara, amma yana da yaƙinin cewa zai iya sauke nauyin da ke gaban sanata yadda ya kamata.

Dangane da ƙwarewarsa, ya ce ya yi aiki a matsayin malamin jami’a na tsawon shekaru, sannan ya yi aiki da hukumomin gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu. Haka kuma ya taɓa zama Manajan Injiniya a tashar wutar lantarki a Legas.

A fannin siyasa kuwa, ya ce ya fara ne tun yana makarantar sakandare, sannan ya shiga harkar siyasa sosai bayan kammala jami’arsa a shekarar 1989.

Hakazalika, Injiniya Darma ya kuma bayyana cewa ya taɓa tsayawa takara kusan sau biyar a matakai daban-daban, ciki har da shugaban ƙaramar hukuma, muƙaman jam’iyya, majalisar wakilai, gwamna da kuma mataimakin gwamna.

Da yake ƙarin bayani kan dalilin yawan tsayawarsa takara, ya ce siyasa na samun ma’ana ne ta hanyar shiga takara da neman goyon bayan jama’a, yana mai cewar “A ganina, tsayawa takara shi ne ginshiƙin siyasa. Ko ka yi nasara ko ka sha kaye, duk yana hannun Allah,” in ji shi.

A ɓangaren biyayya kuwa, ya ce an san shi da biyayya ga shugabanni tuntuni, yana mai cewar ko da a ce yana kan kujera ne, idan manyansa ciki har da gwamnan jihar suka buƙaci ya sauka, zai yi hakan cikin sa’o’i 24.

Injiniya Darma ya karkare da cewar, matakin da ya ɗauka na tsayawa takarar Sanatan hukunci ne na ƙarshe, kamar yadda aka riga aka fara yaɗawa a kafafen yaɗa labarai, yana mai shan alwashin ganin ci gaba mai ɗorewa a ɓangarori daban-daban ga rayuwar ‘yan jihar da kujerar tasa, kamar yadda al’umma suka san shi da aiwatar da hakan ko ba a siyasa ba.

Yanzu da akwai yan takarar kujerar mutane huɗu da suka haɗa da wanda yake ci yanzu Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da Injiniya Muttaƙa Rabe Darma sai Abbas Masanawa da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema wanda hotunan takarar sa ke yawo amma bai fito ya nuna aniyar sa na tsayawa takarar ba.

By ukarofi