Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sanya hannu kan dokar ta-ɓaci kan ‘yan ƙauraye da yan bangar siyasa a cikin garin Katsina.
Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa kafa wannan doka ya biyo bayan ƙaruwar faɗace faɗacen ƙauraye da yawaitar bangar siyasa a faɗin jihar musamman cikin garin Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya kuma bayar da umarnin a riƙa hukunta duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifi nan take.
Matakin na zuwa ne a wani yunƙuri na gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin birnin Katsina.
