Jami’ar Gombe ta ƙaddamar da tsarin yaƙi da cin zarafin jima’i

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jami’ar Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani sabon tsari na hana cin zarafin jima’i, a wani mataki na ƙarfafa tsaro da tabbatar da mutunci a harabar makarantar.

An sanar da ƙaddamar da tsarin ne a wani taro da ya haɗa shugabannin jami’a, ƙungiyoyin fararen hula, masu fafutukar kare haƙƙin mata da wakilan hukumomin gwamnati, inda aka nuna damuwa kan yawaitar matsalar a manyan makarantu.

Da take jawabi, Daraktar Cibiyar Nazarin Harkokin Jinsi ta Jami’ar, Farfesa Aishatu Abubakar Kumo, ta ce sabon tsarin ya tanadi hanyoyi na zamani wajen karɓar ƙorafi, gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifi.

Ta bayyana cewa tsarin ya ayyana cin zarafin jima’i da ya haɗa da kalamai marasa dacewa, taɓawa, ishara da saƙonnin lantarki da ke tauye mutunci.

A cewarta, jami’ar ba za ta lamunci duk wani hali da zai kawo cikas ga ingancin ilimi da tsaron ɗalibai da ma’aikata ba.

“Dole ne nasara a ilimi ta kasance bisa cancanta, ba tare da amfani da iko ko matsayi wajen cin gajiyar wani ba,” inji ta.

Ta ƙara da cewa tsarin zai ƙarfafa ɗa’a, mutunta juna da kyakkyawar mu’amala tsakanin malamai da ɗalibai a jami’ar.

Sabon tsarin ya kuma tanadi hanyoyin kai ƙara cikin sirri, domin kare waɗanda abin ya shafa ko shaidu daga tsangwama ko ramuwar gayya.

Haka kuma, an kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai rika duba ƙorafe-ƙorafe tare da ba da shawarar hukunci bisa adalci, yayin da aka yi gargaɗi kan gabatar da ƙorafe-ƙorafen bogi.

A nata ɓangaren, wakiliyar ƙungiyar Gender Mobile Initiatiɓe, Fatima Abdullahi, ta yaba da wannan mataki, tana mai cewa babban ci gaba ne wajen tabbatar da tsaro da gaskiya a makarantu.

Ta ce tsarin ya ƙunshi hanyoyin kai ƙara masu inganci, kariyar sirri, tallafawa waɗanda abin ya shafa da kuma hukunci mai tsauri ga masu laifi.

Hakazalika, ta gabatar da manhajar “Campus Pal” da za ta taimaka wa ɗalibai wajen kai rahoto cikin sauƙi da samun taimako cikin gaggawa.

Wakilai daga Ma’aikatar Shari’a, NAPTIP da NSCDC sun yaba da shirin, suna mai jaddada buƙatar aiwatar da irin waɗannan tsare-tsare domin magance matsalar gaba ɗaya.

Masu ruwa da tsaki sun buƙaci a ƙara wayar da kai, a ƙarfafa hanyoyin kai ƙara da kuma tabbatar da hukunta masu laifi ba tare da nuna son kai ba.

An rufe taron da sabunta alƙawarin haɗin gwiwa daga dukkan ɓangarori domin tabbatar da aiwatar da tsarin yadda ya kamata, tare da gina jami’a mai tsaro, mutunci da bin doka.

By ukarofi