Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Masana’antu na ƙasa, John Owan Enoh, ya umarci kamfanin Dangote da ya ƙara faɗaɗa ƙarfin samar da sukari na kamfaninsa na DSR zuwa tan 600,000 a duk shekara kafin shekarar 2030.
Ministan, tare da rakiyar Babban Sakatare Janar kuma Manajan Majalisar Bunƙasa Sukari ta ƙasa (NSDC), Kamar Bakrin, ya bayar da wannan umarni ne yayin da ya kai ziyarar duba aiki a rukunin masana’antar DSR da ke Numan, Jihar Adamawa.
Ziyarar na daga cikin jerin rangaɗin dabaru da gwamnati ke yi a sassa daban-daban na ƙasar, bisa umarnin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin hanzarta cimma burin dogaro da kai wajen samar da sukari a Nijeriya.
Ministan ya bayyana cewa adadin sukari da ake samarwa a cikin gida a halin yanzu bai kai ga biyan buƙatar ƙasar da ta kai kusan tan miliyan 1.8 a duk shekara ba.
Ya ƙara da cewa, a matsayin babban kamfani a fannin, DSR na da muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawar aƙalla tan 600,000 kafin 2030 tare da tabbatar da ɗorewarta.
Ya jaddada cewa nasarar wannan fanni na dogaro da yadda manyan kamfanoni kamar DSR ke gudanar da ayyukansu, yana mai yabawa shugaban NSDC bisa ƙwazo da jajircewarsa wajen bunƙasa harkar sukari, amma ya ce dole ne a samu haɗin kai daga kowa domin cimma manufofin Tsarin Samar da Sukari (NSMP).
Ministan ya kuma yaba wa NSDC kan rawar da take takawa wajen sa ido da ƙarfafa kamfanonin da ke fannin, yana mai cewa irin zuba jari, ci gaban ayyuka da kuma girman kayayyakin more rayuwa da ya gani a DSR, musamman sabon shirin masana’antar ton 6000 a rana (TCD), na nuna cikakken jajircewa ga shirin haɗa samarwa daga cikin gida, wato Backward Integration Programme (BIP).
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya a shirye take ta yi aiki tare da kamfanin Dangote domin kawar da duk wata tangarda da ke hana ƙaara yawan samar da sukari a cikin gida.
A yayin amsa tambayoyin ‘yan jarida, Ministan ya bayyana cewa duk da cewa shirin BIP na tafiya yadda ya kamata, har yanzu ana buƙatar ƙara ƙaimi domin cimma manufofin NSMP, musamman ganin yawan buƙatar sukari a ƙasar.
Ya kuma nuna cewa daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta akwai samun jarin dogon lokaci mai sauƙin biya, wanda ake kira patient capital, inda gwamnati ke duba hanyoyin taimakawa kamfanoni wajen samun irin wannan jari.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote, Olakunle Alake, ya tabbatar wa Ministan da cewa kamfanin zai ƙara zuba jari tare da faɗaɗa ayyukansa, yana mai alƙawarin cewa za su cimma burin ton 600,000 kafin shekarar 2030.
A yayin ziyarar, Ministan da shugaban NSDC sun zagaya wuraren faɗaɗa masana’antar, gonakin rake, hanyoyin jigilar kaya da sabbin wuraren noma, tare da duba injinan sarrafa sukari da ajiyar kayayyaki.
